Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya yi bayani akan halin da yankin arewa zai shiga idan kasar nan ta rabe biyu

- Gumi ya yi bayanin ne a wata hira da yayi da jaridar Sun, inda ya bayyana cewa idan kasar ta rabu biyu arewa ce za ta sha wahala

- Ya kara da cewa yankin kudu da basu da matsala tunda su abinda suka sani shine kasuwanci ya san cewa za su daidaita kansu

Legit  ta ruwaito Fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan, Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, yayi gargadi akan cewar Najeriya na iya rabewa gida biyu kuma yankin arewa ne za su fi shan wahala.

Malamin ya ce rikici zai balle a arewa idan hakan ta faru yayin da yankin kudu za su yi kokari wajen daidaita yankunansu.

"Na ga matsala na tunkaro Najeriya, kuma hakan ba karamin illah zai yiwa 'yan Najeriya ba," Gumi ya bayyanawa jaridar Sun.

"Bari na fada muku abinda zai faru da yankin arewa idan har kasar nan ta rabe gida biyu. Yankin kudu maso yamm da yankin kudu maso gabas za su yi kokarin ganin sun daidaita yankunansu, yayin da yankin arewa zai kasance cikin rikici da tashin hankali. Daga yaya zamu iya kawo karshen Boko Haram dake yankin arewa maso gabas? Daga yaya zamu kawo karshen matsalar fulani makiyaya a arewa? Ba zamu iya kawo karshensu ba.


"Maganar gaskiya ma shine, kokarin da yankin kudu suke yi wajen yakarsu shine yake rage musu karfi, amma idan suka tafi suka barmu da su na tabbata arewa ta gama lalacewa kenan.

"Kuma Najeriya za ta zama kamar kasar Lebanon ko Yemen. Babu wanda zai iya kawo karshen matsalar arewa tunda babu wani wanda yake da wannan karfin a arewa.

"Duk mutanen arewa kowa na nuna bangarenci na yare inda hakan ba karamin barazana bace ga kasar nan. Yankin kudu maso yamma suma sun rarrabu amma kuma su basu kaimu rikici ba.

"Za su iya yarjejeniya wajen kawo karshen matsalar dake tsakaninsu, saboda su abinda suka sani shine kasuwancinsu," in ji shi.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top