Daga Maje El-Hajeej Hotoro
*Duk Abinda Ya Shamuwa Watan Bakwai Ne Ya Janyo Mata*
A jiya ne Babban Sakataren Zartaswa na Hukumar Tace Finafinai ta jihar Kano Isma'il Afakallahu ya bayar da sanarwar haramta shirya fim da Miji zai kashe matarsa ko kuma ita ta kashe.
Kisan miji a kwanakin baya ya so ya zama ruwan dare, duk da dai bana tsammanin a finafinan Hausa suka KOYI kisan. A tunanina hukumar ta hana shirya fim ne akan kisan Ma'aurata ne saboda fargabar kada wasu su koya. Idan Gabadaya Kannywood an koma shirya fim ne akan kisan Ma'aurata wannan ba daidai ba ne. Am idan wasu tsiraru sun yi ne domin wayar da kai gami da fito da hanyoyin magance matsalar wannan daidai ne.
Amma maganar gaskiya kamar an bar Jaki ne ana dukan taiki. Domin idan haramta abubuwa za a yi don kada wasu su koya, to fa abubuwan haramtawar suna da yawa. Kawai abinda na yarda shirya Fim mai sunan Fim na DUNIYA ba na Malam Bahaushe ba ne, sai dai kawai a yi abinda za a yi a dan samu na kashewa. Abubuwa da dama sun ci karo da addininmu da al'adunmu.
Misali ko rawa da waka da masu shirya finafinai suka dauka shine fim na daga cikin abinda yan kallo da yawa ke zargin yana lalata music tarbiyyar yara. Gardi iya gardi ya zage ya rika tikar rawa yana rangwada gami da karya kugu yana bin mace yana kwarkwasa wai shi Sarkin Soyayya.
Koyon rawa da waka a wajen 'yan fim wannan abu ne a ZAHIRI da maza da mata suke yi kusan kowane gida amma me ya sa hukumar bata dauke shi a matsayin wata barazana ba?
Sannan wacce gudunmawa Gwamnati da Hukumar ke ba wa masu shirya finafinan wajen inganta Sana'ar? Bugu da Kari hukumar tana da hurumin Hana sa wasu abubuwan a gidajen Talabijin masu zaman kansu?
Wanda a yanzu an fi kallon su fiye da yard ake kallon finafinan Kannywood?
Kuma ko me ya samu Shamuwa watan bakwai ne ya janyo mata. Ga duk wanda ya ga yadda yan fim suke tonon sililin juna a kafar sadarwa gami da yada gurbatattun abubuwa akan su na rashin tarbiyya zai goyi bayan kowane mataki aka dauka a kansu. Sun karkata hankali wajen rikici da gaba gami da gulma a tsakaninsu fiye da kyautata hadin kan juna da raya masana'antar.
©HausaLoaded
Post a Comment