Ai Sharin Dan Allah
Ciwon nono shi ne samuwar wasu kwayoyin cuta acikin nonon mace, wanda ke haddasa ciwo da canja yanayin maman mace ko ya lalata shi gaba daya. Ciwon nono wani lokacin yana janyo ru6ewar nono ko yay sanadin a yanke shi gaba daya
ABUBUWAN DA KE KAWOWA MATA CIWON NONO.

1- Shekaru.
    Idan mace shekarunta suka dan fara yawa, to yana da kyau ta fara daukar matakan kariya daga ciwon nono.
2- Sinadarin 'iyistirogen', idan yay yawa ajikin mace.
3- Fara jinin al'ada kafin mace ta kai shekaru sha biyu, za ta iya gamuwa da ciwon nono.
4- Mace ta zarce shekaru hamsin da biyar tana jinin al'ada, shi ma zai iya janyo mata ciwon nono.
5- Rashin haihuwa. Matan da sam ba su haihu ba, har su ka wuce shekaru talatin, za su iya kamuwa da ciwon nono.
6- Jinkirin haihuwa, idan mace ta dauki shekaru da yawa da aure ba ta samu haihuwa ba za ta iya kamuwa da ciwon nono.
7- Girman jiki. A binciken likitoci, mace mai tsawo da mace mai kiba, sun fi shiga hadarin kamuwa da ciwon nono, musamman masu tarin kitse a jikinsu ko a qugunsu.
8- Gado. Idan iyayen mace suna fama da ciwon nono, to itama zai iya yiwuwa ta yi gado.
9- Idan nono mace guda daya ya ta6a yin ciwo, to zai iya yiwuwa dayanma ya kama ciwo daga baya.
10- Matar da aka ta6a cire mata tsiro a mamanta, yana da kyau ta dinga zuwa asibiti  tana samun shawarwari don gudun kamuwa da ciwon nono daga baya.

ALAMOMIN CIWON  NONO

1) Canjin yanayin girman nono. Haka kawai ki ga nononki ya kara girma ko ya yamutse, ba tare da wani dalili ba.
2) Jin kullutu acikin nono. Za ki ji kamar wasu abubuwa suna tsirowa daga nononki, har suna kara girma.
3) Canjin kalar fatar nono. Za ki ga fatar nonon tana komawa kamar kalar lemin zaqi ko wata kala daban.
4) Canjin kalar fatar kewayen nono (nipple), ki ga fatar wajen ta yi jajawur.
5) Kan nonon mace (nipple) ya zama ya kumbura haka kawai kuma yana ciwo.
6) Fitar wani ruwa kamar ruwan ciwo haka kawai daga nonon mace. Ba sai lallai mai shayarwa, ko da budurwa ce.
7) Radadi da ciwo mai zafi akan nonan da kuma hammata ko da yaushe kuma haka kawai.
8.) Kumburin hammata tsakanin allon kafada zuwa sashin nonan.
9- Jin ciwo mai tsanani idan kika matsa nonon.
RIGAKAFI YA FI MAGANI.

Yadda za ki gane kina dauke da cuta a mamanki, tun kafin ya fara ciwo.
1- Za ki ga wani dan tsiro akan nononki amma ba ya ciwo kuma ba ya zafi, wasu matan ma suna dauka kamar wani abin ado ne.
2- Yana iya farawa da jin ciwo kadan a maman.
3- Ya kan iya farawa da ciwo ko kaikayi a fatar da ta zagaye kan nonon.
4- A wasu matan kuma, kan nonon ne yake fara shigewa ciki, za ki ga kan nono daya ya shige ciki, dayan kuma ba haka yake ba. Likitoci suna ganin idan har kan nonon ya lo6a ciki, to cutar ta fara ha6aka kenan.
5- Wasu ya kan fara da fitar wani ciwo a karkashin maman, wanda zai dinga kara yawa, yana kewaye kasan maman kuma ba lallai ne ya zama yana yin zafi ba.
Karin bayani.
Idan akayi sake ba a dauki mataki da wuri ba, zai iya yiwuwa ciwon yayta  ci daga ciki, har ya taso fatar maman, ya zama gyambo wanda yake fitar da jini da ruwa mai wari.
Zai iya yiwuwa ciwon nono ya fara ta saman fatar, yana kuma iya farawa daga can cikin nonon, don haka da an ji canji to a gaggauta tuntu6ar masana.

MAGANIN CIWON NONO

1) Idan nonon ya fara ru6ewa, yana fitar da miki, to a samu:-
  i) Jan kajiji, cokali daya.
  ii) Baqin kajiji, cokali daya.
  iii) Habbatus saudaa, rabin cokali.
iv) Habbatur Rashad, rabin cokali.
v) Alum, rabin karamin cokali.
vi) Farar wuta, rabin karamin cokali.
vii) Tafarnuwa, Yar kadan.
   Dukkan wadannan abubuwa garinsu za a samu, sai a hada waje daya, a dinga barbadawa akan nonon. Insha Allahu tsakanin kasa da sati daya zai kame. Idan ya kame, sai a kwa6a sauran maganin da man kadanya, ta cigaba da shafawa.
Amma matukar aka yi haka har tsawon sati biyu bai warke ba ko ba a ga wani canji ba, to a gaggauta tuntu6ar masana.
2) Domin kashe kwayoyin cutar daga cikin jiki. A samu:-

i) Girfa, rabin gwangani.
ii) Citta, rabin gwangwani.
iii) SanaMakkiy Cokali biyu.
iv) Garin zogale, Gwangwani daya.
v) Garin Sabara, gwangwani daya.
A hada waje daya, a daka, ta dinga zuba rabin karamin cokali a ruwan dimi, tana sha, kullum sau biyu.
Indai har wannan hadin ya kare ba a ga wani gagarumin canji ba to a je wajen masana, kar a zauna a gida.

3- Kowace mai ciwon nono, ta samu:-
i) Garin Sabara, gwangwani daya.
ii) Garin Sarqaqiya, gwangwani daya.
iii) Garin jan kajiji, Rabin gwangwani.
v) Citta, yar kadan. Sai ta dinga zuba rabin cokali a cikin nono ko a kunu ko a koko, ta na sha, kullum safe da yamma.
4) Ki samu Na‘ana‘a, ki dafa ta, sai ki dinga gasa nonon da ruwan, sau biyu ko sau
uku a rana. Ayi haka kwana hudu ko fiye.
5) A cakuda garin Hulba da ruwan
zafi, sai ki shafa a nonon tun yamma har safe
sannan ki wanke, da safe sai kuma ki shafa man hulba.
6) A samu garin Hulba da Man shanu, sai ki hada, ki kwa6a, ki dinga shafawa, shi ma yana taimakawa sosai.

7) A tafasa ganyen Na'ana'a, sai ki samu hankici ko tsumma, mai kyau, a dinga gasa nonon.
Amma fa matar da take jin kullutu acikin mamanta to dole ta je asibiti ko wajen masana harkar lafiya.

Kada a dauki lokaci mai tsawo a gida, matukar aka jarraba wadannan hanyoyi ba a dace ba.
Ga mai bukatar magungunan hadadde na ciwon nono ko kara girman mama ko rage girmansa,
A tuntube mu a 0813540404408020738307 kota WhatsApp ne N12500. Zamu aiko jihar da ake bukata ta hannun Direbobi,  zaa turamana kudin  a account namu Eco



©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top