Jarumi Aminu Ahlan ya fito yayi magana dangane da lamarin darakta Sunusi Oscar da aka kama, saboda karya doka da yayi

- Ya bayyana cewa wannan rikici da ya barke bashi da alaka da siyasa ko kadan dan haka mutane su daina magana akan abinda basu sani ba

- Ya kuma yi magana akan Aisha Idris, wacce ta fito ta fatattaki Ali Nuhu da shugaban hukumar tace fina-finai Afakallahu

Jarumin fina-finan Hausa Sharif Aminu Ahlan ya fito yayi magana akan rikicin da ya balle a masana'antar Kannywood, wanda ya samo asali bayan kama fitaccen daraktan fina-finan Hausa Sunusi Oscar 442.

Jarumin ya bayyana cewa wannan lamari da ya sa aka kama jarumi Sunusi Oscar bashi da alaka da siyasa, kuma bai shafi kungiyar Kwankwasiyya ko Gandujiyya ba, saboda haka mutane su daina zuzuta lamarin.

Bayan haka kuma jarumin yayi magana akan budurwar nan Aisha Idris wacce ke a kasar Germany, wacce ta dinga tsinewa jarumi Ali Nuhu da shugaban hukumar tace fina-finan Hausa Afakallahu. Jarumin ya bayyana cewa karuwa ce ita aka biya ta don ta zagi su Ali Nuhu din.


Ga abinda jarumin ya ce:

"Jama'a sunana Sharif Aminu Ahlan, dan banyi niyyar yin magana ba akan wannan lamari na Sunusi Oscar, amma ya kamata na fito na tofa albarkacin bakina a kai.

"Bai kamata mutane su dinga sanya siyaya a wannan lamari ba, wannan abu bashi da nasaba da siyasa, magana ake yi ta wanda ya aikata laifi, amma naga wasu suna ta faman zagin Afakallahu da Ali Nuhu, har naga wata karuwar yarinya an sakata tana neman suna a shafukan sada zumunta.

"Babban abinda ya kamata mutane su fara tambaya shine, wane irin laifi Sunusi Oscar ya aikata, ba wai mu zo muna ta faman maganganu ba babu gaira babu dalili. Wannan dai shine ni abinda nake gani dangane da lamarin, ganin ruwanku ne ku dauka ko ku cigaba da abinda kuke yi," inji jarumi Aminu Ahlan.

Idan ba a manta ba dai a cikin wannan makon ne aka kama jarumi Sunusi Oscar, bayan an zarge shi da yin sakin waka ba tare da neman izinin hukumar tace fina-finai ba.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top