A ranar Laraba 14 ga watan Agusta, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya jagoranci bude wani sabon katafaren aiki na ginin titi mai tsawon mita dubu 33 da gwamnatin jihar Katsina ta kammala. 

Gwamnatin jihar Katsina bisa jagorancin gwamna Aminu Bello Masari, ta kammala ginin wannan babbar hanya a kan zunzurutun kudi na naira biliyan 3.3 da manufar saukaka wa manoma wajen fidda amfanin gonakinsu zuwa wajen jihar. 

Babbar hanyar da shiga cikin yankunan Shinkafi, Yandaki, Gafia, Abdallawa da kuma Dankaba, ta ratsa ta cikin shiyoyi 15 dake cikin birnin Dikko da kuma karamar hukumar Kaita a jihar Katsina. 


Mutane da dama sun yi tururuwa ta shaidawa a yayin bude wannan katafaren aiki da aka fara gudanar da shi tun a watan Oktoba na shekarar 2017. An kuma kammala shi a watan Afirlun 2019 da ya gabata.

 Da yake zayyana jawabansa na farin ciki, shugaban kasa Buhari ya yabawa kwazon gwamnatin jihar Katsina da ta kasance mahaifarsa, inda ya ce hobbasan da gwamnatin ke yi ya yi daidai da akidarsa ta kawo mangarcin sauyi a kasar. 

Baya ga kawo sauki na sufuri, shugaban kasar ya ce babbar hanyar za ta taka muhimmiyar rawar gani wajen inganta jin dadin al'ummar yankunan da ta ratsa cikin su. Gwamna Masari ya ce, ba ya ga wannan aiki, a gobe kuma da ta kasance ranar Alhamis, shugaban kasa Buhari zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatinsa ta kammala bayan cin gajiyarsu a hannun tsohon gwamnan jihar, Alhaji Shehu Shema. 

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top