Manyan mata, ko matan da akafi saninsu da suna senior babs a zamanance, mata ne da akasarinsu suna haura shekaru 30 da haihuwa ko auren fari basu taba yi ba.

Irin wadannan matan, mafiya yawansu sunada rufin asirinsu, sunfi karfin matsalolin rayuwansu, basu kuma cika dogaro da abun hannu wani ba. Matane da akasarinsu anfi samunsu da illimi na boko mai zurfi ko dai ma'aikatan gwamnatine su ko na kamfani ko kuma suna harkokin su na kashin kansu.

Senior Babs, matane da suke maida hankalinsu katokaf akan wani abu da suka saka a gaba a lokacinda suke tsakiyar kurunciyarsu, don haka nema auren wuri baya gabansu har sai sun cimma wannan burin nasu kamin suke waiwayo zancen aure. Kuma matane da basu cika zakuwa ko tilastawa kawunansu dole sai sunyi aure ba ko da wani irin namiji.

Duk kuwa da irin kallon da al'uma suke yiwa irin wadannan matan na sun tsufa babu aure, ko kuma ana musu kallon mata ne da suka buga duniya saboda zurfin karatunsu na zamani. A zahirance matane da suke da sauki da kuma dadin zamantakewa na aure kamar yadda bincike ya tabbatar da hakan.

Su dai Senior Babs, ba kowani irin namiji suke aure ba, kuma basu bata lokacinsu wajen soyayyya muddin basu gama fahimtar namiji ba. Dayake sun rika sun tara, kudi ba ya zama ma'aunin amincewa soyayya dasu. Da yake sun yi cudanya da gwagwarmayan rayuwa da mutane daban daban. 

Dadin baki da kalamomin rudu irin na soyayya bai. Sace zuciyarsu. Matane da karamin tarkon yaudara bai iya kamasu.

Matane kamin su amincewa namiji yakan dauki lokaci mai tsawo suna nazarin mutum. Kuma matane da zaran sun amincewa mutum basa canza ra'ayinsu akansa koda kuwa mai zai biyo baya.

Cikin Senior Babs 10 da suka yi aure, bincike ya tabbatar da kashi 1 kadai aurensu ke mutuwa, sauran kaso 9 suna zaman aurene na cike da soyayya, kaunar juna da fahimtar juna. Bincike ya tabbatar da cewa su Senior Babs mata ne masu hakuri da kawaici. Haka kuma ga biyayya da bin umurnin miji, kula da miji da 'yan uwa da abokan miji. Basa cin amanar aure kuma amfani da kudinsu domin yiwa miji hidima shi yafi komai sauki idan ana aurensu.

"Duk da yake na girmi matata, na aureta tanada shekaru 35 ni kuwa inada 40, wannnan bai hanamu zaman aure mai kyau ba. Shekarun mu yanzu 5 da aure, mun haifi yara biyu mace dana miji kuma Wallahi sai dai idan sharri zan mata amma banda matsala da ita tunda muka yi wannan auren" Usman Ali a lokacinda yake amsa tambayan masu bincike.

"Matata ta girmemini da shekara guda, tafini karatun boko, tafini samun kudi, a gidan kanta nake aurenta. Ta sameni da aurena da kuma 'ya'yana. Wallahi babu abunda zata gudanar a rayuwa muddin ban amince dashi. Duk yadda take son abu idan nace baza ayi baza a yin ba kuwa. Kullum cikin sabuwar soyayya da samata albarka nake yi" Jamilu Yakubu.

"Babu irin surutun da ba ayi ba a lokacinda zan auri matata. Wasu abokaina na cewa suke ban taba aure ba mai zai kaini aure 'yar shekaru kusan 40. Har wajen iyayena aka kaini kara, amma dana fahimtar da iyayena akan shifa zaman aure kwanciyar hankali da fahimtar juna ake bukata ba karanci shekaru ba sai suka bani hadin kai. A yau dinan da muke wannan hira shekarunmu 7 da aure. Munada yara biyu maza, muna cikin kwanciyar hankali da rufin asiri na rayuwa. 

Abokaina da suka auri masu karancin shekaru sun rabu dasu amma ga tawa muna tare kuma kullum sai zama yarinya take yi. Don haka babu abunda zance sai yiwa Allah godiya daya albarkaceni da wannan baiwar Allah". Abdulrazaq Isah.
Akasarin mazajen da akayi hira dasu dai kusan zancen guda ne. Cikin mazajen 10 da aka yi hira dasu masu auren irin wadannan matan guda biyu ne suka nuna basu dace da wannan auren ba. Sai dai guda biyu sun nuna cewa muddin zasu sake wani auren irin wadannan matan dai zasu auro domin sunfi sauki sarrafawa a zamantakewa na aure.
"Wato auren Senior Babs aure ne da yake cike da maturity a ciki. Ita dai ba karamar yarinya bace bare kullum sai ka rika daurata akan hanya. Duk abunda ya kamata takeyi kamin ma ace mata yi. Gogayyar rayuwa yasa ta fahimci iyakanta a matsayin mace da kuma naka iyakar kai mijinta. Macece idan taga zaka kasa zata tallafa maka. Haka kuma duk abunda ta hango zai cutar da kai zata ankarar da kai. A lokacin data bata maka tasan hikimar shawo kanka. A lokacinda ka dadadamata tasan salon yadda zata yi domin nunamaka farin cikinta.
"Mata ne da burinsu kadai a lokacinda suka yi aure subi mazansu sau da kafa, bil hakki da gaskiya babu cuta babu cutarwa. Senior Babs basa nunuku bare daukar zuga ko gulma. Basa shiga tsabgar daba tasu bane. Haka kuma idan kana da wasu matan suna baiwa wadannan matan naka girmansu yadda ya kamata" . Ta bakin Farfesa Idris Mustapha daya jagoranci binciken.

Tsangayar Malam


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top