SIFFAR WANKAN JANABA

بسم الله الرحمن الرحيم

Tambaya:
Yaya ake yin wankan janaba?

Amsa:
Wankan janaba tana da siffofi guda biyu;

(1) Yanayi da ke isarwa na wajibi, 
(2) Da kuma siffa cikakkiya ta mustahabbi([1]).

Amma siffar da ta ke isarwa ga wanda yayi ta kuma ta wajibi: Itace Bawa ya game jikinsa da ruwa tun daga farkon farawa tare da niyya; Ma'anar wannan: Shine bawa ya game jikinsa da ruwa ta kowace fiska yaga dama tare da niyya. Haka zai isar wa mutum; Yayi niyya sai yayi nitso cikin wani kududdufi ko kuma kogi; ta yadda ruwan zai zama ya game jikinsa; Idan ya aikata haka tare da niyya to ya tsarkaka daga janaba.
Amma ita kuma siffa ta biyu cikakkiya ta mustahabbi Itace:
Na farko: Bawa ya wanke tafukansa guda biyu sau uku gabanin tsunduma su cikin ruwa.
Na biyu: Sai ya sanya hannunsa cikin ruwa don ya wanke al'aurarsa da duk wurin da dauxar janaba ta riga ta tava.
Na uku: Sannan sai ya wanke hannunsa da qasa ko da sabulu don gusar da dauxar janaba da ya tava da hannunsa.
Na hudu: Sai kuma ya yi alwalarsa cikakkiya irinta sallah; ma'ana: Ya kurkuri baki, da shaqa ruwa a hanci, ya wanke fiskarsa, sau uku, da hannayensa biyu zuwa guiwowinsu, sau uku, ya kuma shafi kansa da kunnuwa, sannan sai ya wanke qafofinsa sau uku uku.
Na biyar: Sai kuma ya wanke kansa sosai, yana mai shigar da 'yan yatsunsa cikin tushen gashin kansa; Idan har yayi zaton cewa ruwan ya shiga tushensu to sai ya kwara ma kansa kamfata uku.
Na shida: Daga nan; Sai ya wanke sauran jikinsa da ruwa sau xaya, yana mai farawa da saman jikinsa, har ya taho qasa.
Na bakwai: In har kuma ya so zai iya jinkirta wanke qafarsa a yayin alwalarsa har sai ya zo qarshen wankarsa gabaxaya, sai ya koma gefe don wanke qafofinsa.
Waxannan bayanan zasu bayyana cikin hadisan dake tafe:

Na farko: Hadisin Maimunah (RA), ta ce:

"وَضَعْتُ لِرَسُولِ اللهِ r غُسْلاً وَسَتَرْتُهُ فَصَبَّ عَلَى يَدِهِ فَغَسَلَهَا مَرَّةً، أَوْ مَرَّتَيْنِ -قَالَ سُلَيْمَانُ: لاَ أَدْرِي أَذَكَرَ الثَّالِثَةَ أَمْ لاَ-، ثُمَّ أَفْرَغَ بِيَمِينِهِ عَلَى شِمَالِهِ فَغَسَلَ فَرْجَهُ، ثُمَّ دَلَكَ يَدَهُ بِالأَرْضِ أَوْ بِالْحَائِطِ، ثُمَّ تَمَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ، وَغَسَلَ وَجْهَهُ وَيَدَيْهِ، وَغَسَلَ رَأْسَهُ، ثُمَّ صَبَّ عَلَى جَسَدِهِ، ثُمَّ تَنَحَّى فَغَسَلَ قَدَمَيْهِ، فَنَاوَلْتُهُ خِرْقَةً فَقَالَ بِيَدِهِ هَكَذَا، وَلَمْ يُرِدْهَا" ([2]).

Ma'ana: (Na sanya wa Manzon Allah –SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- ruwan wankansa, na kuma suturce shi, sai ya zuba wa hannunsa sai ya wanke shi sau xaya ko sau biyu, -Sulaiman Al-a'amash ya ce: Ban sani ba ya faxi wanke hannu a karo na uku ko a'a-, Sa'annan sai ya zuba ruwa daga hannun damansa i zuwa "hagu" xinsa sai ya wanke "gabansa", sa'annan sai ya xauraye hannunsa da qasa ko da katanga, sa'annan sai ya kurkuri baki ya kuma shaqa, ya wanke fiskarsa da hannayensa, kana ya kuza ruwa a sauran jikinsa, sa'annan ya koma gefe ya wanke qafofinsa guda biyu. Matar manzon Allah Maimunah ta ce: Sai na miqa masa tsumma don tsanar da jiki, amma sai ya karkaxe ruwa da hannayensa; bai buqaci tawol ba). 
A kwai kwatankwacin wannan hadisin daga A'ishah (RA), wanda kuma shi ne:
Hadisi na biyu: Hadisin A'ishah (RA) wanda Imamul Bukhariy da Muslim suka rawaito shi.
ta yadda ya zo a cikinsa:

عَنْ عَائِشَةَ، قَالَتْ: «كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا اغْتَسَلَ مِنَ الْجَنَابَةِ يَبْدَأُ فَيَغْسِلُ يَدَيْهِ. ثُمَّ يُفْرِغُ بِيَمِينِهِ عَلَى شِمَالِهِ فَيَغْسِلُ فَرْجَهُ، ثُمَّ يَتَوَضَّأُ وُضُوءَهُ لِلصَّلَاةِ، ثُمَّ يَأْخُذُ الْمَاءَ فَيُدْخِلُ أَصَابِعَهُ فِي أُصُولِ الشَّعْرِ، حَتَّى إِذَا رَأَى أَنْ قَدْ اسْتَبْرَأَ حَفَنَ عَلَى رَأْسِهِ ثَلَاثَ حَفَنَاتٍ، ثُمَّ أَفَاضَ عَلَى سَائِرِ جَسَدِهِ، ثُمَّ غَسَلَ رِجْلَيْهِ» ([3]).

Ma'ana: (Manzon Allah –saw- ya kasance idan ya zo yin wankan janaba; ya kan fara da wanke hannunsa guda biyu, sannan sai ya kwara ruwa daga hannunsa na dama zuwa ga hagu don ya wanke farjinsa, Sannan sai ya yi alwalarsa irinta salla, sannan sai ya xauki ruwa sai ya shigar da 'yan yatsunsa cikin tushen gashin kansa, idan yaga cewa ya isar da jiqajiqan ruwa to sai ya xibi kamfata uku, Sannan sai ya kwara ruwa ga sauran jikinsa, Sannan sai ya wanke qafofinsa guda biyu". Wannan hadisin da wanda ya gabace shi, sun yi bayanin siffar wankan manzon Allah (sallallahu alaihi wasallama).
A dunqule; dangane da cikakken yanayi ko siffar wanka: To shi ne, Bawa ya wanke hanayensa, sa'annan ya wanke farjinsa, da duk gunda dauxa ta tava, sa'annan ya yi alwala alwalarsa irin ta sallah, sa'annan ya xauki ruwa a hannunsa don ya tsettsefe gashin kansa da shi, yana mai shigar da yatsunsa a cikin tushen gashin kansa; don ya jijjika fatarsa, sa'annan ya xebi kamfata uku don wanke kansa, kana ya kwara ruwa a sauran jikinsa.
Kuma ba wajibi ne mace ta warware gashin kanta a wankan janaba ba. Amma hakan wajibi ne akanta a wankan haila; saboda hadisin Ummu Salamah (RA), ta ce: Na ce: Ya manzon Allah lallai ni mace ce da nake xaure gashin kaina; Shin zan warware shi don wankan janaba? Sai ya ce:

"لا، إِنَّمَا يَكْفِيكِ أَنْ تَحْثِي عَلَى رَأْسِكِ ثَلاثَ حَثَيَاتٍ، ثُمَّ تُفِيضِينَ عَلَيْكِ الْمَاءَ؛ فَتَطْهُرِينَ" ([4]).

Ma'ana: (A'a; Ai zai ishe ki kawai ki xebi kamfata guda uku ki kwara akanki, sa'annan sai ki kwara ruwa a jikinki; sai ki zama kin yi tsarki).

Walhamdu lillah!

([1]) SHI YANAYI DA KE ISARWA GA WADDA YA YI AIWATAR DA SHI SHINE: Wankan ya kunshi wajibai kawai. YAYIN DA SHI KUMA CIKAKKEN WANKA shi ne ya kunshi wajiban da kuma mustahabbai. 
([2]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 266), da Muslim (lamba: 317). 
([3]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 272), da Muslim (lamba: 316). 
([4]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 330).

By sani ahalusunnah


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top