Idan yarinya ta bi maza ta lalace ta fara shaye shaye sata dss ka da iyaye su ɗauka kawar da ita a gabansu su mata aure zai nutsar da ita a'a su miƙe ne wurin gyara tarbiyyan da ya ɓaci kafin miƙa ta ga wani, domin idan har ba su gyara munanan halayenta ba to ba za su daidaita da namijin da a ka bata ba. 

Iyaye maza Ina kira a gare ku don Allah ku mayar da hankali wurin tarbiyyan mace domin ita mace a na yi mata abubuwan da zai taimaka wurin cire idanunta a kan abun hannun wasu saboda wasu yaran kwaɗayi da rashin samun gata ya ke kai su ga zina, ka kula da wadannan:

1. Yin mata ɗinkuna domin mu mata mu na son ganin a na ji da mu.

2. Siya mata takalmi, hijjab da underwears domin wata in ka ga fatarin da ƴarsa ke sanyawa sai ka tausaya mata wani ma rabonsa da siya mata tun na suna duka mahaifiyar ne ke ƙarma ƙarman siya. 

3. Siya mata pad na tare jininta duk wata ko ka ba ta kudin siya domin yawanci da tsumma su ke tarewa ko duk abun da su ka samu kuma ya na kawo mugun infection in ba a kulawa. Na ga yara da yawa da in lokacin jinun su ya kusa su ke fadawa tunani saboda ba su da abun tare jinin which is very wrong. 

4. Siya mata kayan kwalliya su hoda, jambaki, gazal ko a nan a ka tsaya yayi, siya mata man shafawa daban ka da a na cakuɗata da qanninta har ma ka siya mata dan jaka qarama wanda a ke zuba kayan Kwalliya. 

5. Sanya mata kati komin qantarsa idan tana da waya da bata ɗan kudi lokaci lokaci.

6. Kokarin siyo abun kwadayi a gida jefi jefi a na ci da ita. 

7. Yi wa ƴaƴanka nasiha lokaci lokaci, su wance kun ga ina iyakan kokari na kulawa da ku don Allah duk abun da ku ke buqata ku sanar mun in ba za ku iya faɗa min da baki ba ku turo ta text in kun kasa ga mahaifiyarku nan ku sanar mata. Ku yi haquri da rayuwa da abun ku ke samu ku cire ido daga abin hannun wani duk abun da ku ke so in bai fi qarfina ba zan yi iya kokarin samar mu ku da shi. 

8. Ka fadawa mahaifiyarsu da jawo hankalinta sosai a kan ta daina hantaran ƴaƴanta musamman mata su daina yin musu abubuwa tamkar ba su su ka haife su ba, su rinqa jan su a jiki da nuna musu soyayya da jin matsalolin su da lura da canjin walwalar su. Wata hantarar mahaifiyarta ke sanyata zama sadist ta dauki baqin ciki da ɓacin rai har zuwa gidan mijinta. 

Yawancin mu hausa Fulani soyayyar mu ga ƴaƴanmu a baki ne ko lokacin da su ke qanana amma su na fara girma sai mu nesanta da su wanda kuma a lokacin ne ya kamata a jawo su a jiki a sa ido domin sun fara shiga shekarun balaga kuma shi ne mai hatsari kafin hankali ya zo. 

Lalle iyaye ku na bada gudunmuwa sosai wurin rashin sauqe nauyi da tattalin ƴaƴa, a kan samu jarabta da yaro mara jin magana amma yawancin lalacewar tarbiyyan yanzu na rashin kulawa da saka ido da tayar da su a kan tarbiyyan Islam ne da soyayya. Mu ji tsoron Allah kuma mu ji tsoron ranar da za a tambaye mu a kan kiwonmu, Allah Ya sa mu dace Ya taya mu riqonsu.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top