Mun samu daga shafin Rariya ta facebook
Nasabarsar ta bangaren mahaifinsa: Muhammad(saw) dan Abdullahi, dan Abdul-Mutallib, dan Hashim dan Abdul-Manaf, dan Kusayyi dan Kilabi… nasabarsa (saw) madaukakiya tana tukewa zuwa ga Annabi Adam (as) a tsatson masu sujadah da tsarki.

Nasabarsa ta bangaren Mahaifiyarsa: Ita ce Amina ‘yar Wahabi, dan Abdul-Manaf dan Zuhrata dan Kilabi… nasabarsa ta fuskar mahaifinsa da mahaifiyar ta hadu wajen Kilab zuwa ga Annabi Adam da Hauwa(as).

Wadanda suka rene shi: Abdul-Mulib, Halimah As-Sa’adiyya, da Abu Talib.

Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.

Lakabinsa: Al-amin, Al-mustafah…

Sunayensa da suka zo a cikin Kur’ani mai girma: Khatamin-nabiyyin, Al-ummi, Al-muzzammil, Al-muddassir, An-nazir, Al-mubin, Al-karim, An-nur, Anni’ima, Ar-rahma, Al-abdu, Ar-ra’uf, Ar-rahim, As-shahid, Al-mubasshir, An-nazir, Ad’da’i…

Tarihin haihuwarsa: An haifi Monzon Allah(saw) a Ranar Jumu’ah, 17 Rabi’ul Auwal Shekarar Giwa (571 M) (bisa mash’hurin zance daga Ahlul-Bayt(as) (amma a wata ruwayar an haifeshi(saw) ranar Litinin 12 Rabi’u-auwal).

Inda aka haifesa: Makka.

Tambarin zobensa: Muhammadur-Rasulullah!

Tsawon rayuwarsa: shekaru 63.

Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23.

Aiko shi: An aiko shi a Makka, 27 Rajab; yana dan shekara 40.

Koyarwar sakonsa: ya zo don daidaito tsakanin dukkan halitta da ‘yan’uwantaka da rangwame, sa’annan ya kafa shari’a madaukakiya da dokoki na adalci da ya karbo daga wajan Allah(swt), su kuma Musulmi suka karba daga gare shi.

Mu’ujizozinsa: Mu’ujizarsa madauwamiya ita ce Qur’ani, amma wadanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa; ba zasu kirgu ba, misali, tsagewar wata.

Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a boye shekara 3, ya kuma kira su a bayyane shekara 10.

Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi’ul Auwal, bayan shekara 13 daga aikosa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai; gare shi da kuma Sahabbansa.

Yakokinsa: Allah ya yi wa Manzo(saw) izinin yakar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi dauki ba dadi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar, Uhud, Al-khandak(Ahzab), Khaibar, Hunaini…

Matansa: Khadija ‘yar Khuwailid (as) ita ce matarsa ta farko. Sauran su ne; Saudatu ‘yar Zami’a, A’isha ‘yar Abubakar, Gaziyya ‘yar Dudan(Ummu Sharik), Hafsa yar Umar, Ramla ‘yar Abu Sufyan (Ummu Habibia), Ummu Salama ‘yar Abu Umayya, Zainab ‘yar Jahash, Zainab ‘yar Huzaima, Maimuna ‘yar Al-Haris, Juwairiyya ‘yar Al Haris, Safiyya ‘yar Huyayyi dan Akhdab.

‘Ya’yansa: Abdullah, Al-Qasim, Ibrahim, Fatima(as). A wani kaulin akwai Zainab, Ruqayya da Ummu Kulsum.

Ammominsa maza: 9 ne, su ‘ya’yan Abdul-Mudallib ne: Al-haris, Zubair, Abu Talib, Hamza, Al-Gaidak, Dirar Al-muqawwam, Abu Lahab da Abbas…

Ammominsa mata: Su 6 ne daga iyaye mata daban- daban sune: Amima, Ummu Hakima, Barra, Atika, Safiyya, Arwa…

Khadiminsa: Anas dan Malik…

Mawakinsa: Hassan dan Sabit, Abdullahi dan Rawahata, Ka’abu dan Malik…

Ladanansa: Bilal Al- Habashi, Abdullahi dan Ummul-Maktum da Sa’ad Al-kirdi.

Tarihin Shahadarsa (wafatinsa): 28 Safar 11 H.

Wajan da ya yi shahada: Madina.

Inda aka binne shi: Madina a dakinsa madaukaki, mai alfarma.

Annabi Muhammad(saw) shine karshen Annabawa(as) kuma addininsa shine Musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari’arsa zata wanzu har zuwa Qiyama kuma ita kadai ce shari’ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa karshen rayuwar Duniya da cigaban rayuwar Lahira.

Annabi Muhammad(saw) abin koyi ne ga dukkan Duniya baki daya, dukkan mutanen duniya idan suna son alkhairi ga kawukansu; to dole ne su bi tarfarkinsa(saw); su yi koyi da kyawawan halyensa(saw) da kuma sanin tarihinsa da siffofinsa(saw):

Annabi Muhammad(saw) dan Abdullah da Amina, an haife shi a Makka ranar juma’a goma sha bakwai ga watan Rabi’ul-awwal, bayan bullowar Al-fijir a shekarar giwa…

An aiko Annabi Muhammad(saw) da sako a 27 ga Rajab bayan yana dan shekara 40 yayin da Jibril(as) ya sauka gareshi daga wurin Allah(swt) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makka ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaq. Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makka a lokacin akwai jama’a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da sakon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi; yana cewa da su: “Ku ce babu abin bauta sai Allah ku rabauta”. A lokacin tunda mutanen Makka mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka rika yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk lokacin ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce; “Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni”.

Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane kalilan, na farkonsu Imam Ali(as), sannan sai matarsa KHadizah(as) sannan sai khalifa Abubakar…

Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madina, yayin da suka yi yawa sai karfinsu ya dadu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah(saw) da shari’arsa mai sauki mai hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madina har sukafi dukkan duniya da addini na sama da wadanda ba na sama ba.

An samu yakoki masu yawa a Madina; dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga makiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan Musulmai, kuma Annabi(saw) a kowne lokaci yana zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne darangwame, don haka ne ma adadin wadanda ake kashewa daga bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa tamanin da wani abu, wato; wadanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba.

Mutuwa Mai Zafin Gaske; Tun lokacin da aka aiko Annabi(saw) da sako har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu(as) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji(swt) a hankali a hankali har littafin Qur’ani ya ciki a cikin shekaru ashirin da uku, sai Manzo(S.A.W) ya yi umarni da a hada shi kamar yadda yake a yau din nan.

Manzo(saw) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu’amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.

Bayan cikar addini da na Imam Ali(as) a matsayin khalifansa na farko, sai Allah ya saukar da ayar: “A yau ne na kammala mukuaddininku, na cika ni’imata gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini”. Sai Annabi (saw) ya yi rashinlafiya mai sauki, sai dai yayi tsanani har sai da ya hadu da Ubangijinsa a 28 ga watan safar na 11H.

Kuma Imam Ali(as) shi ne ya yi masa wanka da sallah da binne shi a dakinsa a Madina inda kabarinsa yake yanzu.

Annabi (saw) ya kansace abin koyi ne; a rikon amana, ikhlasi, gaskiya, cika al-kawari, kyawawan halaye, girma, kyawawan dabi’u, baiwa, ilmi, hakuri, rangawame, afuwa, sadaukantaka, tsentseni, takawa, zuhudu, baiwa, adalci, kaskan da kai, jihadi…

Jikinsa (saw) ya kasance kololuwa wajen kyau, daidaito, dacewa… kuma fuskarsa kamar wata ne mai haske da ya cika, zuciyarsa da ruhinsa sun kai matuka wajen kamala, mafi kamalar halaye, ladabi, dabi’a… sunnarsa tana haske kamar rana a tsaka-tsakinta.

A takaice; Annabi(saw) ya tattara dukkan wata dabi’a mai kyau, girma, daukakada, ilimi, adalci, takawa, iya tafiyar da al’amuran duniya da na lahira, wadanda babu wani mahaluki da yake da irinsu.

Wannan shine Annabin musulmi kuma wannan shine addinin Musulunci, addininsa(saw) shine mafificin addinai, littafinsa shi ne mafifcin littattafai, domin shi: “Barna ba ta iya zo masa ta gabansa da ta bayansa, abin saukarwa ne daga mai hikima abin yabo”.

Allah(swt) ya karawa Annabi Muhammad(saw) daraja da dauka, ya samu a cetonsa, ya biya mana bukatunmu; albarkacinsa(saw) da Ahlul-bayt(as)!!

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top