Daya daga cikin Dattawan da suka kafa masana'antar fina finai ta kannywood, Dan'azumi Baba Cediyar yangurasa wanda  aka fi sani da Kamaye a cikin shirin Dadin kowa na tashar Arewa24 Northflix ta ruwaito.

ya tabbatar da cewa yan fim ne da kansu su ke kashe harkar fina finan Hausa,.

Ya Kara da cewa duk kokarin da su ka yi a baya domin ganin samuwar harkar fim da kuma dorewar  ta, amma ga shi duk tsawon lokacin da masana'antar ta yi har yanzu ba za ace ga wani cigaba da ta samu ba.

Dan`azumi Baba Jarumi, Darakta kuma Furodusa ya Bayyana Hakan ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilin mu.

In da ya ke cewa "Har yanzu wannan harkar ana yi mata kallon ta cin abinci, amma gaskiya harkar fim ta wuce maganar cin abinci, don ana yin arziki a cikin ta sosai, Sai dai mu da yake ba mu da tsari tun da farko don haka sai aka samu kai a cikin irin wannan yanayi.

Wannan ya sa yanzu da za ka duba harkar idan za ka ce an samu ci gaba to ba ta wuce ta kayan aiki ba. Ya kuma Kara da cewa." Mune muka samar da kannywood, mun fara ta don nishad kawai, ba mu taba zaton za ta girma haka ba.

Ganin fara samun kafuwar harkar a wancan lokacin yasa muka Kara rike ta a matsayin sana,a , sai muka samu matsala na rashin shugabanci mai karfi aka barta sakaka ba doka.

Rashin dokar yasa ba ta samu wani tsari ba tun farkon tafiyar, aka bar kofa bude ko wani kare da doki zai iya shigowa ba babba ba yaro kuma a lokacin shekarun mu sun ja, don haka Sai ya zama ba bu girmamawa yaran ba mu suke kallo ba kawai dai abin da suka ga dama suke yi.

Toh da yara sun shigo suna ganin sun fara samun kudi sai su fara raina kowa  ba wanda ya isa ya tsawatar musu, babu wanda ya isa ya fada Masu suji to a kan haka ne masana'antar fim ta samu kanta a cikin halin da take ciki a yanzu "

Mun tambaye shi ko me ya sa a yanzu da suke a matsayin wadanda suka kafa harkar ba za su shigo ba su tsawatar?

Sai ya ce" to a yanzu dai zan iya cewa abu ne mai wahala, tun da su yaran ba sa ganin girman kowa, don haka babu wani gyara da za ka kawo a cikin mutanen da ba su ma yarda da kai a matsayin mai tsawatarwa ba, kowa yana ganin ya isa, idan ka ga an nemi dattawa to wata rigimar ce ta taso kuma ake ganin idan har manya ba su shiga ba lamarin ba zai yi kyauba , don haka sai a nemo mu duk in da muke, amma fa daga matsalar ta wuce ba za ka Kara ji an neme mu ba.”

Ko ya za a yi a samo mafita? Ita  ce talbayar da wakilin mu ya yi masa

“Gaskiya hanya daya ce shi ne a dawo kan tsari, Dan wasa ya san shi dan wasa ne, Darakta ya san shi Darakta ne, haka shi ma Furodusa, kowa ya tsaya a matsayin sa kuma a yarda duk wanda Allah ya ba shi basira mutum ne mai daraja a cikin jama'a, ta haka ne za a dauki hanyar gyaran masana'antar,  Amma dai na san, in dai ba haka aka yi ba, to muna ji muna gani harkar nan gaba za ta fi karfin mu.

Ko wani dan  fim ya shiga taitaiyin sa, ya kula tun kafin mu kasa amsa sunan mu a matsayin fim, saboda nan gaba zata fita daga hannun mu Sai dai mu gani anayi, Allah shi kyauta ba ma fatan hakan. Ko da kuwa ace bayan ran mu ne.” ijni Dan'azumi Baba

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top