Maganar Cewa Duk Abinda Annabi Bai Yi Ba Bidi'a Ne Korarre, Ba Maganar Malaman Musulunci Bane, Magana Ce Wadda Wahabiyawa Suka Kirkira


Maganar cewa duk abinda Annabi bai yi ba, bdi'a ce abin korewa, magana ce ta Wahabiyawa wanda suka kirkire ta domin su buga kan jahilai.

Babu inda ya tabbata a Sunna ko a ijama'in malamai cewa duk abinda Annabi bai yi ba korarre ne a cikin addini, koda abin ya kunshi kyawawan abubuwan da musulunci ke horo da a aikata, kamar karatun Alqur'ani da hadisi da ciyarwa da shayarwa da sauran su.

Kasancewar ba duk abinda Annabi saw bai yi bane bidi'a, yasa manyan Imaman mazhabobi kamar  Imamu Malik da Imamu Shafi'i da malaman da suka biyo bayansu irinsu Imamul Suyudi da Imamu Hajarul Asqallani da Imamul Gazali suka karkasa abinda Annabi bai yi ba (Bidi'a) zuwa kaso biyar kamar yanda suka karkasa Ahkamul Shar'i, hukunce hukuncen shari'a zuwa gida biyar, ga rabe raben bidi'a nan kamar yanda Shehu Usman Dan Fodio, shima ya kawo a cikin littafinsa mai suna Ihya'ul Sunna :

*Bidi'a wajiba
*Bidi'a haramtaciyya
*Bidi'a mustahabbiya
*Bidi'a Makaruhiya
*Bidi'a Mubahiya

Dole se da aka bi ta hanyar bidi'a sannan addinin musulunci ya daure, saboda Shehu Usman Dan Fodio ya bayyana cewa rubuta Alqur'ani a takarda da rubuta littafan ilimomin addini da shari'a da kirkiran mazhabobi duk bidi'oi ne wadanda Annabi SAW bai yi ba, amma dole yasa aka kirkire su saboda idan ba'a yi su ba addini ba zai iso ma wadanda suka zo daga baya ba. Kaga kenan ba kowani bidi'a bane abin ki, malamai suna lura da abinda bidi'an ya kunso ne, idan ya kunso abubuwa masu kyau se ya zama bidi'a me kyau, idan kuma ya kunso abubuwa marasa kyau se ya zama bidi'a mara kyau.

Saboda haka bidi'ar da ta kunshi taruwa a yi karatun Alqur'ani da hadisai da yabon Annabi SAW da ciyarwa da shayarwa bidi'a ce me kyau, mustahabbiya wanda ake kwadayin samun lada idan aka aikata ta, kamar yanda Malamai irinsu Imamu Suyudi da Imamu Gazali da Imamu Hajarul Asqallani da sauran tarin malaman musulunci suka bayyana.

Allah ya ganar da mu amin...

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top