Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Daya daga cikin jarumai da suka dade ana fafatawa da su a cikin masana'antar finafinai ta kannywood, Adam M Adam wanda aka fi sani da Maigaskiya, ya bayyana manyan jaruman masana'antar a matsayin mtsalar da harkar fim take fuskanta.

Jarumin ya bayyana Hakan ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilin mu Mukhtar Yakubu dangane da irin rawar da jarumai suke takawa wajen ci gaban masana'antar, in da ya fara da cewar.

"To shi jarumi za a iya cewa shi ne kashin bayan harkar fim, saboda shi ake gani a cikin akwatin talbijin don haka masu kallo ba su san kowa ba sai jarumi, wannan ta sa duk wani abin yabo da na suka yana karewa ne a kan jarumi".

Mun tambaye shi ko me ya sa ba a ganin sa yanzu a finafinai kamar a lokacin baya?

Sai ya ce" To abu biyu ne, na farko na samu dama na tafi na Kara karatu, na biyu kuma matsalar ita harkar fim din musamman manyan jarumai, da su ke ganin su ne harkar fim din, idan babu su ba za a yi ba.

Don haka su ke daukar wa kan su su ne masu yi, Idan aka kawo Musu fim da sunan wanda ba sa so, Sai su ce lallai sai an cire sunan wane a cikin fim din sannan za su yi, An sha kira na fim amma sai daga baya na ji shiru, kuma sai in ga fim din ya fita.

Idan na yi bincike, sai na samu labarin wani jarumi ne ya sa aka cire suna na, Sun kasa gane cewa Allah ne kawai ya ke yi, Ya kamata su gane cewa da yawa wadanda aka yi wa wulakanci a harkar nan yanzu su ne suka zama wasu.

Da alama dai wannan abin yana damun ka sosai?

Gaskiya ne, domin ba sau daya ba ba sau biyu ba, an sha yi min haka, kuma wannan abin ba daidai ba ne.

Don kana ganin lokacin ka ne ka rinka tauye wani saboda wata manufa ta ka, Don haka ina kira ga abokan harkar mu na fim musamman ma manyan jaruman da suke ganin idan babu su ba harkar, da su ji tsoron Allah a kan Lamar in su, domin idan yau su ne gobe ba su ba ne".

Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top