Bayyan ko wane ya fadi albarkacin bakinsa shine wannan darakta ya fitar da wani jawabi mai hikima.


"Assalamu Alaikum

Da fari ina mai Baku hakuri masoya da abokan Sana,a wanda suka hanani bacci cikin daren nan badon komai ba sai don irin damuwa da son ganin wannan masana,anta ta hade kanta don ciyar da Al'umma gaba.
Hakika kowanne Dan Adam Tara yake Bai cika goma ba MANZON ALLAH S. A. W. shi kadai bawan Allah daya cika cuf dai dai wadaida wanda babu wata tawaya ta zahiri ko ta badini gareshi, sallallahu alaihi wasallam.
Amma mu sauran bayi Allah ya halicce mu da naqasu kala kala dalilin wannan magana inaso na sanar da masoya ADAM ZANGO Abokin Sana,a tane kuma munyi harkokin arziki iri iri tare wanda mun amfana da juna bana manta wa tun film darajar jarumi bata wuce 6k ko 5k ba muke aiki tare dashi cikin kwanciyar hankali har zuwa sanda Allah ya daukakeshi ya tashi daga USHA ya koma ADAM A ZANGO😂 na cigaba dayi masa biyayya a matsayin wanda Allah ya daukaka fiye da ni kuma Hakan Bai Hana shi girmama abotar dake tsakanin mu ba saboda haka wannan rashin fahimta na dauketa gazawar Dan Adam kamar yadda na fada a farko Dukkan nin mu mun Gaza Amma kuma Allah ya nusar damu da wuri kuma ina fatan zamu yafi juna.

NASIHA 1

Nasiha ta farko zanyi ta ne Akan kaina ta kin koyi da wani HADISI na Manzo sallalhu alaihi wasallam ASTAGFURULLAH inda shugaba yake cewa ASSABRU INDA SADMATUL UULA ma,Ana HAKURI YAYIN FUSHIN FARKO da nayi aiki da wannan HADISI to da Hakan bata faru ba.

NASIHA 2

zanyi ta ne Akan ADAM ZANGO kullum akwai wata addu,a da Manzo yake yi Akan mashawarta NAGARI ga ma,,bota MULKI da DAUKAKA ya kamata ka yawaita yinta, sannan muzama masu tuntuba Akan abinda bamu da tabbas kamar yadda ALQUR,ANI YACE idan mabarnaci yazo muku da labari to kada kuyi shiru kubayyana domin shirun zai iya Sawa ku wayi gari Kuna masu nadamar aikin da kuka aikata sadaqallahul azeem

Allah yasa mu dace KA YAFE MIN NIMA NA YAFE MAKA IDAN HAR KAYIMIN WANI ABU.
 @adam_a_zango"

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top