Wanka shine gamai dukkan jiki da ruwa tare da cuɗawa,
Musulunci addinin tsarki ne da tsafta da ado da kwalliya,
Allah ya ce yana son masu tuba da masu tsarki
Manzon Allah saw yace : Tsarki shine rabin imani.
Yace:  Allah mai kyau ne yana son kyau.
Don haka babu ƙazanta da dauɗa da datti, a musulunci kada wani ya ɗauka zama cikin najasa ko datti alama ce ta imani da son Allah,
Manzon Allah saw yace:  Haƙiƙa Allah baya duba zuwa ga surorin ku da kamanninku yana duba ne zuwa ga ziciyoyinku da aiyukanku. Muslim
Ana  amfani da yin alwala ko wanka idan zaa gabatar da ibadar da baa yinta sai da tsarki,

YADDA AKE WANKA
Yadda ake yin wankan janaba da wankan ɗaukewar jinin haila da jinin biƙi duka iri ɗaya ne sai a niyya suka bambanta,
Yadda ake wanka ya kasu kashi biyu
Na ɗaya idan mutum zai yi wankan ibada ya sami ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, kamar Yadda ya gabata, sai yayi basmala a farko sai ya wanke hannun sa sau uku, sai ya wanke gabansa, bayan ya wanke gaban sa, sai ya kuma wanke hannun sa saboda da ƙazanta daya taɓa, sai yayi alwala yadda yakeyin alwalar sallah, sai ya wanke kansa sau uku ya zuba ruwa ya cuɗa koina ya tabbatar ruwa ya ratsa gashin sa ya tarar da fatar kansa, daganan sai ya wanke kafaɗarsa ta dama zuwa ƙafa, ya dawo ya wanke ta hagu zuwa ƙafarsa ya tabbatar ya wanke duk wasu gurare masu loko kamar hammata da cibiya da matsematsi, da bayan gwiwa da ƙarƙashin ƙafa, da dunduniya da tsakanin yan yatsun ƙafa, da baya, da wajan kaushi da Faso, domin abin da ake buƙata a wajan wanka shine gamai jiki da ruwa, a tabbatar koina ya sami ruwa tare da niyyar wanka idan wannan ya samu wanka ya cika, yadda ake buƙata.
Kashi na biyu na wanka shine, mutum yayi niyar wanka kawai, ya dulmiya a cikin ruwa, ko ya shiga cikin kwamin wanka, ko ƙarƙashin shaya ko ruwan sama ko cikin kogi yu cuɗa jikin sa koina ya sami ruwa shikenan ya gama wanka, domin an sami mahimman abubuwa guda biyu da suke tabbatar da ingancin wanka sune niyya da kuma gamai jiki da ruwa.

ABUBUWAN DA SUKE JAWO WANKA
Abubuwan da suke jawo ayi wankan ibada sune
Na ɗaya fitar maniyyi a cikin bacci ko a farke, daga namiji ko mace ta hanyar lafiya da jin daɗi, saboda hadisi Idan ruwa ya fita ayi wanka,  Muslim da Abu Dauda, wato idan ruwan maniyyi ya fita ayi wankan janaba.
Idan Mutum yayi mafarki yana saduwa da mace amma da ya farka babu alamar fitar maniyyi babu wanka akansa.
Idan mutum yayi mafarki yana saduwa da mace bayan ya farka sai yaga maniyyi a jikin sa wajibi yayi wanka,
Idan ya tashi daga barci sai yaga maniyyi a jikin sa amma bai yi mafarkin saduwa ba, wajibi yayi wanka saboda samuwar maniyyi a tare da shi, wanda fitar sa tana jawo wanka.
Idan mutum yaga maniyyi a jikin kayansa amma bai tuna lokacin da yayi mafarki ba sai yayi wanka ya rama sallar da yayi daga lokacin da ya kwanta wannan baccin da yayi mafarkin.
Dalili na biyu shine saduwa tsakanin mace da namiji ya shigar da gaban sa a cikin gaban mace, wajibi suyi wanka ko da maniyyi bai fito ba.
Manzon Allah saw yace yace Idan Kaciya biyu ta haɗu wanka ya wajaba, ko maniyyi bai fito ba.
Idan mutum ya rungumi matar sa suka yi wasa kawai babu saduwa kuma maniyyi bai fito ba babu wanka akan su saboda rashin dalilin wanka guda biyu fitar maniyyi ko Kuma shigar da kaciyar namiji cikin farjin mace. Idan baa sami ɗayan biyu ba babu wanka.
Idan maniyyi ya fitowa mutum bayan yayi wanka wasu malamai suna ga babu buƙata ya sake wanka, na farko ya isa. An ruwaito daga Zuhriy da Hasanul Basriy sunyi Fatawa ga wanda maniyyi ya fito masa bayan ya gama wanka cewa babu buƙatar ya sake wanka. Duba Musannaf na Ibn Abi Shaibah 1/139.
Idan ya maniyyi ya fitowa mutum ta hanyar rashin lafiya ko wata larura ko aka yi masa wata allura domin a ɗauki maniyyi a jikin sa, duka wannan babu buƙatar yin wanka, saboda rashin fitar maniyyi ta hanyar sha'awa.
Idan mutum ya ga wani abu a jikin sa, amma yana shakka maniyyi ne koba maniyyi bane sai ya shinshina idan ya sami yakini ko zato mai zato mai ƙarfi cewa maniyyi sai yayi wanka domin ya fita daga kokwanto.
Haramun ne mutum ya sadu da matar sa tana cikin jinin al'ada ko jinin biƙi, ko ya sadu da ita ta dubura, amma idan  ya keta shari'a yayi, sai yayi wanka kuma yayi nadama yayi kaffara ya tuba.
 Dalili na uku da yake jawo wanka shine Ɗaukewar jinin al'ada, idan mace ta gama jinin al'ada ta tabbatar ya ɗauke har taga alamar Ɗaukewar sa, sai tayi wanka kamar yadda ya gabata a baya yadda ake wankan ibada.
Dalili na huɗu shine jinin biƙi, idan mace ta haihu, jinin da yake biyo baya ya ɗauke sai tayi wanda, kamar yadda ya gabata, siffar yadda ake wanka na ibada.
Dalili na biyar idan Allah ya arzuta mutum da shiga addinin musulunci,ya wajaba yayi Wanka, na ibada, kamar yadda ya gabata da niyyar ya shigo musulunci, saboda wani ya musulunta Manzon Allah saw ya umarce shi yayi Wanka,
Dalili na shida Wanka ranar Juma'a domin yaje sallah cikin tsarki da Tsafta,
Dalili na bakwai idan mutum ya mutu ayi masa wanka kafin a binne shi, sai waɗanda shari'a tace baa yi masu wanka, kamar wanda yayi Shahada a filin daga fi sabilillah.
Akwai wasu abubuwa da suke jawo ayi wanda amma ba wajibi ba masali
1 Wanka ranar idi guda biyu na sallar ƙaramar salla da babbar salla idan za a tafi idi ayi wanka tukunna baihakiy  ya ruwaito daga Sayyadina Aliyyu.
2  wanka domin shiga haramar aikin hajji ko umra, idan alhaji ya isa miƙati anso yayi wanka kafin ya ɗora ihramin sa, wannan wanka shima mustahabbi ne. Sahihu tirmiziy 664.
3 wanka domin tsayuwar arfa an so ranar tsayuwar arfa, ayi wanka kafin a isa filin arfa, ko idan an isa kafin rana ta yi zawali, saboda hadisin da aka ruwaito daga Sayyadina Aliyyu wani ya tambaye shi gamai da yin wanka sai yace masa kayi wanda duk sanda Kaga dama, sai mutumin yace, ina nufin na ibada wanda ba wajibi ba sai yace masa kayi wanka ranar Juma'a da ranar arfa da ranar babbar salla da ƙaramar sallah,Baihaƙiy ya ruwaito shaik Albania ya inganta shi a irwa'ul galil. 1-177.
 4 wanka domin shiga garin macca, saboda an ruwaito daga Abdullahi ɗan Umar, idan ya iso macca sai ya kwana a wani guri da ake kira zi ɗuwan, bayan ya wayi gari sai yayi wanka sannan ya shiga garin Macca, kuma yace haka ya gani Manzon Allah saw ya yi. Bukhari da Muslim suka ruwaito.
 5 wanka ga wanda ya yi wa mamaci wanka, saboda hadisin Abu Huraira yace Manzon Allah saw yace duk Wanda yayi wa mamaci wanka shima sai yayi wanka, wanda kuma ya ɗauke shi ya yayi alwala. Sahihu Tirmiziy 791.
Yin wanka da wanda ya farfaɗo daga suma. Saboda haka ta faru da Manzon Allah saw, kuma yayi wanka bayan ya farfaɗo kamar yadda yazo a cikin Bukhari da Muslim.
 6.yin wanka ga wanda ya sadu da iyalansa kuma ya na buƙatar sake komawa anso yayi wanka a tsakanin haka., an ruwaito daga abu Rafi'i yace Manzon Allah saw ya kewaya matan sa a dare ɗaya, yanayin alwala a tsakani . sai aka tambaye shi mai ya sa ba za ka wadatu da wanka ɗaya ba? Sai yace haka yafi tsafta da daɗi da kuma tsarki. Sahihu Sunan ibn Majah 486.
7  wanka ga mace mai larurar zubar da jinin cuta, duk sanda za ta yi sallah sai tayi wanka. Daga Ummu Habibah bnt Jahash ta gamu da larura na jubar jinin cuta sai Manzon Allah saw ya umarce ta da yin wanka duk sanda za tayi salla. Sahihu sunan abi Dauda 269.
8. Anso idan. Mutum ya binne gawar wani makusancinsa wanda ba musulmi ba, yayi wanka, saboda hadisin Sayyadina Aliyyu da Manzon Allah saw ya umarce shi da yin wanka, bayan ya gama binne Abu Ɗalib Abu Dauda da Nisa'iy duba Jamiul usul na Shaik Shuab Ar'na'uɗ.
Idan mutum yana da janaba sai ya zama ranar Juma'a ce kuma ta dace da ranar idi, idan yayi wanka ɗaya tare da niyyoyin duka waɗannan wankan ya isa, a wajan wasu malamai.
Idan jinin haila ya ɗaukewa mace kuma ga janaba tare idan ta yi wanka ɗaya, da niyya biyu ya wadatar ba sai ta yi wanka biyu ba. A fatawr wasu malaman..
Ya halatta mace da majin ta suyi wanka tare kamar yadda Manzon Allah saw yake wanka da iyalansa a wasu lokutan.
Mal. Aɗa'u yace ya halatta ga mai Janaba yayi ƙaho, ya yanke farce ya aske gashin kansa, ko da bai yi alwala ba.
Idan mai janaba yana so yayi bacci, an so ya yi Wanka, ko alwala ko taimama, amma wankan yafi.
Baya Halatta ga mai janaba yayi abubuwa biyar
1ɗaukar Alkurnani mai girma, sai idan akwai wata larura, saboda hadisin kada wani ya taɓa Alkur'ani mai girma sai yana da tsarki.
Imam Malik ya ruwaito daga Abdullah Ɗan Umar.
2 kada yayi Ɗawafi yana da Janaba sai yayi Wanka saboda hadisin Ɗawafi da Ɗakin Allah kamar sallah yake sai dai ana magana a cikin sa. Nasa'iy da Tirmiziy suka ruwaito.
3 Zama a cikin masallaci, ga mai Janaba, sai idan da Wata Larura, Saboda Aya ta 43 a cikin suratu Nisa'i.
Gumin jikin mai Janaba ba najasa bane, Bukhari da Muslim.
Kafin mai janaba ya ci abinci anso yayi ya wanke hannu ko yayi alwala.
Baya halatta ga mai janaba yin salla, ko zama cikin masallaci ko Ɗawafi, ko karanta Alkur'ani Mai girma har sai yayi wanka tukunna, sai domin neman tsari, ko da wani dalili na shari'a.
Sharaɗin wanda guda takwas ne su ne, Niyya, Musulunci, Hankali, Tantancewa, ruwa mai tsarki, gusar da duk abin da zai hana ruwa taɓa fatar mai wanka. Ɗaukewar jinin haila ko jinin biƙi, kafin ayi wanka.
FARILLAN WANKA.
Farillan sune yin niyya a farkon wanka na biyu gamai jiki da ruwa, da gusar da dukkan abinda zai hana ruwa shiga jiki, wasu malamai suna saka shaƙa ruwa da facewa a cikin Farillan wanka. Kuma wajibi idan. Mutum zaiyi wanka ya nemi wajan da babu wanda zai ga al'aurar sa ko tsiraicinsa, in ba iyalinsa ba.

Ƙadan daga cikin littafin Salla daga cikin shirin Tambaya mabuɗin ilmi wanda zai fito kwananan insah Allah.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top