A watannin bayan nan ne wata kura ta tashi a masana’antar Kannywood tsakanin jaruma Hadiza Aliyu Gabon da Amina Amal a kan abunda a ke zargin Gabon din da neman Amal da lalata, Wanda hakan ya janyo cecekuce tare da juya akalar kafafen sada zumunta zuwa masana'antar Kannywood a wancan lokacin.
A cikin kudurin da Amal ta gabatar a gaban kotun ya hada da bukatar kotu da ta umarci Hadiza Gabon da yin abubuwa guda hudu wadanda su ka hada da ba ta hakuri a rubuce, kuma a wallafa ba da hakurin a shafukan manyan jaridu na kasar nan guda biyu, kuma kotu ta hana ta ko wani nata ci mata mutunci a nan gaba, sannan kuma ta biya ta diyyar Naira Miliyan 50 a matsayin haddi na bata mata suna da ta yi.
Lauyoyi 15 ne su ka saka hannu a takardar da ita Amal din ta gabatarwa da kotu a wancan lokacin ta karkashin kamfanin lauyoyi na A A Umar (SAN) dake unguwar farm center a Kano.
Bayan tsawon watanni da aka shafe ana shari'ar a yanzu dai alkali ya fatali da karar a sakamakon rashin gamsassun hujjoji da Amina Amal ta yi wajen shigar da karar ta ta. Domin haka ne a zaman kotun na ranar juma'a 8 ga watan Nuwamba ta kori karar, wanda hakan ya kawo karshan wannan Shari'ar.
Hakan ya sa mu ka yi kokarin jin ta bakin Hadiza Gabon amma ba ta ba mu damar magana da ita ba sai dai ta hada mu da lauyanta Barista Sadiq Kurawa, Inda yake cewa
“Da farko dai alhamdulillahi mun samu nasara a kotu, inda kotu ta ce masu kara ba su da wata kwakkwarar sheda da hujja akan Karar mu da su ke yi da kuma tarar Naira 50 Million da su ke nema.” Inji Lauyan nata
Me za kace game da bata sunan da aka yi maku, Kana tunanin za ku daukaka kara ne domin ku nemi hakkin ku ko kuma kun yafe?
Sai yace "ba bu wani zance bata suna tunda anje kotu idan mutum ya zo ya ce ka mai laifi har ta kai ga zuwa gaban hukuma kuma aka je aka duba aka ga ba a kama ka da wani laifi ba. Ka ga ai nasara ce babba. Tun kafin ma abun ya yi nisa munyi ta kokarin mu ga anyi sulhu amma abun ya faskara, kuma munyi ta kiran zama kafin a shiga kotu har sau uku amma ita mai Karar ba ta taba zuwa ba, to tun daga nan ne mu ka gane cewa akwai wani abu a kasa tunda mun yi iya kokarin da za mu yi amma ba su ba mu hadin kai ba.” In ji Barista Kurawa
Wane kira zaka yi wa mutane idan sun tsinci kansu a cikin wani yanayi makamancin haka?
“To ni dai kiran da zan yi wa mutane shi ne Indai har akwai hujja mai karfi wacce za ta kare mutun. Ina ganin zuwa kotu ba laifi ba ne, saboda shari'a sabanin hankali ce. Inji Lauyan Hadiza Gabon.
©HausaLoaded
Post a Comment