Wasannin da ka buga yau na zagaye na 16 na cin gasar kofin zakarun turai duk sun kare canjaras, Lyon ta rike Barcelona a gidanta babu ci, duk kungiyoyin biyu sun samu damarmakin cin kwallaye amma bata shiga ba, golan Lyon, Anthony Lopes ne ya zama gwarzon dan wasan.


Liverpool da Bayern Munich ma haka aka tashi babu wanda yaci kwallo duk da dai cewa Bayern Munich din ta fi yin wasa me kyau akan Liverpool din dake gida.

Post a Comment

 
Top