Fadar shugaban kasa ta hannun me magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu ta kara jaddada maganar da shugaban kasar yayi ta kisan masu yunkurin satar akwatin zabe ko kuma tada husuma a rumfunan zabe.
Sanarwar tace maganar shugaba Buhari ta kashe wanda suka zo satar akwatin zabe tana nan kuma za'a aiwatar da ita akan duk wanda yayi yumkurin aikata laifin.
Sanarwar tace masu satar akwatunan zabe suna zuwane da shiri na musamman dauke da makamai su saka rayuwar mutane a cikin hadari sannan su kashe na kashewa dan su saci akwati, dan haka duk wanda yayi yunkurin saka rayuwar masu kada kuri'u cikin hadari to zai rasa tashi rayuwar.
Sanarwar tace, a lokacin da shugaba Buhari yayi waccan magana yana sane da tsaron jama'ar Najeriya a zuciyarshi kuma kamata yayi ace yabanshi akayi akan wannan batu maimakon suka.
Ya kuma yi magana akan masu sukar kalaman na shugaban kasa inda yace masu sukar kamar 'yan jam'iyyar adawa na PDP ne wanda sun riga sun gama shiri tsaf dan yin magudin zabe ta hanyar sace akwatunan zabe, dan haka su sani cewa shugaba Buhari ba zai yadda da shirmen nasu ba.
Garba Shehu yace idan mutum ba halayyarshi bace satar akwatin zabe kalaman na shugaban kasa basu shafeshi ba.
Post a Comment