Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya jawo hankalin jami'an tsaron soji da cewa aikinsu shine kare iyakokin kasarnan amma ba shiga harkar zabe ba.

Atiku ya bayyana hakane a wajan taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP da ya wakana a babban birnin tarayya, Abuja.

Atikun na mayar da martanine akan kalaman da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi na cewa duk wanda aka samu da satar akwati a bindigeshi da kuma amincewa da hukumar soji ta yi cewa zata bi umarnin shugaban kasar.

Atikun yace shi dai burin siyasarshi be yandda da zubar da jinin kowane dan Najeriya ba, Atikun dai ya ari wannan kalamine daga gurin tsohon shugaban kasa,Jonathan sannan ya bukaci shugaba Buhari da ya janye wancan kalami nashi na cewa a harbe masu satar akwatin zabe shima ya fito ya bayyana cewa burin shi na siyasa ne amince da zubar da jinin 'yan Najeriya ba.

Sannan ya bukaci jami'an tsaro da su taimaka wajan kare kundin tsarin kasarnan.

Post a Comment

 
Top