Wallahi an rainawa matasanmu ajawali. Shekara da shekaru ba ku ba su takardar sama musu aikin yi ba sai takardar “nomination” na kwamitin kamfe. Shi kuma shawarakin sai ya dora a fesbuk yana wage baki yana so ka ce masa “Congratulations”


Ya kamata mu yi karatun-ta-nutsu. Idan takardar aikin CBN ne ko FIRS ko NNPC ko NLNG ko TETfund wallahi ko kyallinta ba ma gani domin ‘ya ‘yansu suke rabawa.
Kaico!

Daga Jaafar Jaafar

Post a Comment

 
Top