Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ya shawarci 'yan Najeriya akan idan suka fita kada kuri'arsu gobe, Asabar su yi tunanin kodai su zabi shugaban da zai sa su ci gaba talauci a yayinda masu kudi kuma su yi ta kara kudancewa ko kuma su zabi wanda zai kawo daidaito tsakanin talakawan da masu kudi.

A'isha Buhari ta bayyana hakane jiya, Alhamis a babban birnin tarayya, Abuja inda ta rabawa mata da matasa kayan sana'o'i dan dogaro da kansu.

Post a Comment

 
Top