Lura da hakori na daya daga cikin hanyoyin dakan kara fitar da kima hadida kamalar
mutum.

Duk yadda mutum yakai ga iya kwalliya hadida kwarewa wurin daukar wanka daxarar yagaxa tafannin kula da hakoransa saikaga gabadaya kwalliyar ta lalace, dankuwa yagaxa tafannin bawa hakoransa kulawar data dace.

Danhaka wannan wata hanyace daxata dawowa mutum kima, martaba hadida darajar hakoranki/ka koda kuwa hakoran sunyi irin baki ko tsatsa tacikine haka kuma yakan yaki kwayoyin cutar dakan haifarwa mutum warin baki.

1-STRAWBERRIES;
Kinemi ganyen itacen strawberry kiyankashi kanana-kanana kidinga cuda hakoran dashi, yana sanya hakora haske sosai haka kuma yana kore dattin dake makalewa ajikin hakora, hakanan yana sanya baki fitar da iska me dadin kamshi.

2-LEMON ZAKI(ORANGE);
Kisamu lemon xaki mekyau meruwa kiyanka kimatse ruwan sannan ki guntsi ruwan abakinki sannan kisanya brush kidinga diddirxawa lungu da sako sannan kixubar kiwanke da ruwa.

Yanasa hakora suyi kashar kamar kankara.

3-LEMON TSAMI(LEMON)
Kisamu lemon tsami kiyanka ki matse ruwan sannan ki sanya abakinki kiwanke kowane lungu da saki na bakin, yana fitar da duk wani dabbara-dabbara dakan makale a hakori.!!!

Post a Comment

 
Top