Fitaccen jarumin masana’antr shirya fina-finan Hausa (Kannywood), Abba El-Mustapha, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su san cewar akwai rayuwa bayan zabe, don haka kar su bari siyasa ta raba kan su.
–
El-Mustapha, wanda aka fi sani da ‘Abba Ruda’ ya yi wannan jan hankali ne a wani rubutaccen sako da ya fitar a shafin sa na sada zumunta (Instagram) yayin hutun krshen mako.
“Kada ka bari siyasa ta had aka rigima da kowa. Ka yi siyasa cikin mutunci da girmama wa don akwai rayuwa bayan zabe,” a cewar jarumin.
Jarumin ya kara yin kira ga ‘yan Najeriya a kan su daina dage wa a kan lallai sai an bi ra’ayin sun a siyasa domin kowa da nasa ra’ayin.
“Kar ka tursasa wa kowa bin ra’ayin ka, kowa yana da nasa. Idan ka girmama ra’ayin wani, kai ma sai a girmama na ka. Banga da ta’addancin siyasa bas u dace ga duk wani mutum mai hankali ba ,” a cewar Abba Ruda.
Sannan ya yi kira ga matasa da su bari ‘yan siyasa na amfani da su domin tayar da husuma da tarzoma a lokutan yakin neman zabe da lokacin zabe da ma bayan sa.
“Ku daina bari ‘yan siyasa su na amfani da ku wajen tayar da rigima a cikin al’umma. Ba don cigaban kasa su ke amfani da ku ba, su na amfani da ku ne domin biyn bukatr kan su. Allah ya ganar da mu, ya sa mu dace ,” in ji jarumi Abba Ruda.
Post a Comment