Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee wadda tana daya daga cikin na gaba-gaba wajan tallata dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ta caccaki masu barin jam'iyyar ta PDP a 'yan kwanakinnan wai dan sun ga alamar cewa Atiku ba zai yi nasara a zabe me zuwa ba.

Ummi tace ashe dama mulki sukewa ba Atikun suke so ba, ta kara da cewa to gara da aka yi walkiya suka gansu kuma gobe ma rana ce, ita dai tace tana so da kaunar Atikune ba dan zai ci mulki ba ta kara da cewa da dan mulki ne da ta je APC tunda sune ke da rantsatstsar kujerar shugaban kasa.

Ummi ta kara da cewa ko da Atiku be ci zaben 2019 ba zai iya cin na 2023 tun da Buharin ma ai ba sau daya ya fito ya ci zaben ba.




Post a Comment

 
Top