Zuwa ga Shehin mu. Ina so ne kayi tsokaci akan yadda cousins suke cin amana. Wallahi matata ce na kamata da cousins dinta akan gadonmu. Saboda yadda na aminta da shi a matsayin dan uwanta yake shigomana gida.

Na gods.

Salam,

Malam Tonga gaskiya inaso ne kayi rubutu akan cousins. Mijina ne yayiwa cousin dinsa ciki. Tana yawan zuwa gidanmu kuma a gabana zanga suna wasan banza amma ban taba kawo wani abu a raina ba. Ashe suna lalatq da juna. 
Dama aurenta zai yi bazai bata mini rai ba. Kullum idan na fita na barsu babu abunda suke yi sai iskanci. Wasu lukutan ma ina gidan ashe suke yi. Bayan hakan ya kasance ne na fahimci mata da dama suna fama da irin wannan iskancin da sunan cousins. Don Allah kuyi rubutun da zaku wayarwa al'uma kai akan wannan dangantakar ta cousins.
Bissalam.

Da fatan kana lafiya. Allah Ya kara basira amen.
Budurwa nake nema mun yi kusan shekaru uku tare. Saura watanni uku a daura mana aure sai na gano sau uku dan uwanta ma'ana cousin dinta yana mata ciki. Yanzu haka bai wuce kwanaki biyar ba suka zubba da cikin sun dauka ban sani ba. 
Gaskiya irin wannan cin amanar da 'yan mata suke yi da cousins dinsu yayi yawa a gari. Akwai bukatar fahimtar da mutane wannan lamarin. Kuma a gaskiya rubutunka yana cikin irin wadanda ake katuwa dasu. Shi yasa na rubutumaka wannan inbox din saboda ka taimaka kaima.
Idris Isa daga Abuja.

Da ire iren wadannan dunbin wasikun ne naga ya kamata muyi bayani akan cousins. Ni kaina nasan cin amanonin da cousins suka yi da damar gaske. Ko yanzu haka akwai wani kwamachalan da aka nemi shawarata yadda za a warware matsalar. 
Da yake masu karatu basa jimre karanta dogon rubutu, shi yasa wani lokacin nake gutsure rubutuna na kawosu kashi kashi saboda kada na gunduri masu karatun wadanda saboda amfaninsu ake yi. Wannan rubutun ma zamu kawo shi kashi kashi ne. Da fatan za a amfana.

Dan Wa da Dan Kani. Ko 'Yar Ya da 'Yar Kanwa ko abunda yayi kama da hakan shi ake kira a turance da Cousin.
Kabilu da dama sun danbaka wasa tsakanin wadannan 'yan uwan biyu. Ko dai wasa tsakanin mace dana miji ko kuma mace da mace ko maza muddin dai 'ya'yan yaya da kanine ko ya da kani da dai sauransu.
Amma a tsari na addini musamman musulunci, akwai auratayya tsakanin mace da mijin da 'yan uwa suka haifa. Hakan kuwa ya tabbata ne daga fadin Alkur'ani mai tsarki da girma. Inda ya ambato irin mazan da aka haramtawa mace aure, wanda kuma 'ya'yan 'yan uwan mahaifa basa ciki. Kamar yadda yazo a suratul Nisa'i aya na 22 zuwa 24.
Haka ma a suratul Ahzab aya na 33 zuwa 50, Allah Ya umurci ManzonSa Annabi Mohammadu (SAW) da yana iya auren 'ya'yan kawunansa na ko wani bangare. Wandannan ayoyin basu takaita akan Annabi kadai ba amma ga dukkan muminai maza da mata.
A bisa koyarwar addini babu inda aka yarda cousins su rika wasa irin wanda alada ya zo dashi. Wasanni irin na baka dana hannu, guje-guje harma da doke-doke. Wannan wasan da al'ada ya jawo tsakanin 'yan uwan, ya jawo barna sosai a tsakanin masoya harma da ma'aurata. Ganin yadda cin amana da yaudara yake samuwa da sunan cousin dinane.
Da dama a msulunce sun manta cewa cousins basa cikin muharramai da aka haramta musu aure. Sai suke sakaci da ganganci baiwa cousins wani matsayi da basu dashi a cikin tsari na zamantakewan aure da soyayya.
Zamu ci gaba.

Tsangayar Malam.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top