Yayin wata tattaunawa da Kamaye yayi da tashar Dala FM ya bayyana cewa iya tsawon shekarun da masana’antar tayi, sune suka tsugunna suka haife ta, amma rikon sakainar kashin da sukayi mata ya haifar da koma baya a masana’antar.
Sai dai yanzu zamani ya kawo cigaba wajen kayan aiki na zamani a cewar Kamayen.
Wannan dai na zuwa ne a lokacin da manazarta ke kallon masana’antar na fama da tangal-tangal wajen rashin tabbataccen jagoranci.
©HausaLoaded
Post a Comment