A Ranar 7 ga Watan Disamban 2019, Babban Limamin Masallacin nan na Al-Furqan da ke Garin Kano, Bashir Aliyu Umar, ya yi magana a kan raba masarautun jihar Kano a hudunar Legit ta ruwaito.

Dr. Bashir Aliyu Umar ya ba gwamnatin Mai girma Abdullahi Umar Ganduje shawara a kan kirkirar sababbin Sarakuna. Hakan na zuwa ne bayan kudirin kafa masarautu ya zama doka.

Babban Malamin na Hadisan Manzon Allah da Fiqhun Malikiyyah ya yi tir da yadda doka ta ba gwamna damar zaben wadanda za su rika nada Sarki, ganin irin shaidar da aka yi wa ‘yan siyasa.

A cewar Shehin, masu nada Sarki sun samu wannan daraja ne dalilin Jihadin musulunci da kuma hijira da mubaya’ar da Kakakininsu, su ka yi wa Shehu Danfodio a can shekarun baya.

Limamin ya na ganin ba daidai ba ne siyasa ta nemi ta yi katsalandan a cikin sha’anin Sarakuna. Malamin ya jawo hankalin jama’a a game da yadda gwamnoni su ka rusa kananan hukumomi.

Malamin ya nuna cewa bai kamata gwamnatin jihar Kano ta Dr. Abdullahi Ganduje ta kawo abin da zai raba kan jama’a tare da jawo sabani ba. Bashir Umar ya nemi gwamnati ta duba maslaha.

Bugu da kari, Limamin ya bayyana cewa Sarakunan da ake da su a kasar Arewa, Sarakuna ne Musulunci ba na gargajiya ba, don haka ya ce bai kamata a taba mutuncin addinin Musulunci ba.

Dr. Umar ya yi kira ga Mai girma gwamnan Kano wanda ake yi wa lakabi da Khadimul Islam, ya cigaba da yi wa addinin Musulunci hidima kamar yadda aka san shi, ya guji ruguza Musulunci.

Wannan huduba da aka gudanar a Masallacin Al-Furqan ta yi daidai da abin da Sheikh Aminu Daurawa ya fada game da barka masarautun Kano, inda ya ce hadin-kai ake nema ba rabuwa ba.A Ranar 7 ga Watan Disamban 2019, Babban Limamin Masallacin nan na Al-Furqan da ke Garin Kano, Bashir Aliyu Umar, ya yi magana a kan raba masarautun jihar Kano a hudunar Juma’a.

Dr. Bashir Aliyu Umar ya ba gwamnatin Mai girma Abdullahi Umar Ganduje shawara a kan kirkirar sababbin Sarakuna. Hakan na zuwa ne bayan kudirin kafa masarautu ya zama doka.

Babban Malamin na Hadisan Manzon Allah da Fiqhun Malikiyyah ya yi tir da yadda doka ta ba gwamna damar zaben wadanda za su rika nada Sarki, ganin irin shaidar da aka yi wa ‘yan siyasa.

A cewar Shehin, masu nada Sarki sun samu wannan daraja ne dalilin Jihadin musulunci da kuma hijira da mubaya’ar da Kakakininsu, su ka yi wa Shehu Danfodio a can shekarun baya.

Limamin ya na ganin ba daidai ba ne siyasa ta nemi ta yi katsalandan a cikin sha’anin Sarakuna. Malamin ya jawo hankalin jama’a a game da yadda gwamnoni su ka rusa kananan hukumomi.

Malamin ya nuna cewa bai kamata gwamnatin jihar Kano ta Dr. Abdullahi Ganduje ta kawo abin da zai raba kan jama’a tare da jawo sabani ba. Bashir Umar ya nemi gwamnati ta duba maslaha.

Bugu da kari, Limamin ya bayyana cewa Sarakunan da ake da su a kasar Arewa, Sarakuna ne Musulunci ba na gargajiya ba, don haka ya ce bai kamata a taba mutuncin addinin Musulunci ba.

Dr. Umar ya yi kira ga Mai girma gwamnan Kano wanda ake yi wa lakabi da Khadimul Islam, ya cigaba da yi wa addinin Musulunci hidima kamar yadda aka san shi, ya guji ruguza Musulunci.

Wannan huduba da aka gudanar a Masallacin Al-Furqan ta yi daidai da abin da Sheikh Aminu Daurawa ya fada game da barka masarautun Kano, inda ya ce hadin-kai ake nema ba rabuwa ba.

©HausaLoaded

Post a Comment

Top