KOH MACE DA SHEKARUNTA SU YAWAITA.....
Dr: Barrah Almadany
Tabbas akwai dinbin alfanu wajen auran bazaura a zaman takewar aure. Kadan daga ciki. Zamu so mu koma zamanin manzan Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi.
Watarana daya daga cikin sahabbinsa yazo yana kanshin tirare. Sai manzon Allah yace. Wane yanaji kana kanshin tiraren angwanci ? Sai wannan sahabin manzon Allah yace ya ma'aikin Allah haqiqa na angwance ne.
Sai manzon Allah yace shine ba gayyata.? Sai sahabbin yace ya ma'aikin Allah na Lura aiyuka sun yawaita agareka. Sai manzon Allah. Yace kwarai da gaske haka zancenka yake. Shin matar budurwa ce ? Koh bazaura ?
Sai sahabin yace masa ya ma'aikin Allah bazaura ne. Sai manzon Allah yace inama budurwa ce.? Sai sahabbin yace ya ma'aikin Allah hakika Babana ya mutu ya barni da kannai kananu. Sai manzon Allah yace kwarai da gaske haka zancen yake.
Kadan daga cikin abin da zamu tsinta a cikin wannan hadisi. Magana ta wannan sahabbi Mai daraja. Hakika idan kana bukatar samun mace Mai kwarewa a zaman takewar aure sai bazaura. Domin ita budurwa tana bukatar horaswa na musamman akan lamarin zaman takewa.
#FIFIKON #BAZAURA
1:IYA GIRKI Bazaura bata bukatan sai an koya mata yadda ake girki
2:IYA TARERAYA: mace bazaura bata bukatan a koya Mata salo na kisisina na shagwaba
3IYA KWANCIYA :mace bazaura bata bukatar a koya Mata salo salon da ake kwanciya DA miji.
4LALASHIN MIJI:mace bazaura bata bukatar a koya Mata yadda zata lalashi Dan lelenta wato mijinta.
5:HAKURIN BABU :mace bazaura tana da juriyan abinda miji ya kawo🤣🤣
6:TAUSAYI :bazaura tana da tausayi.
7:SUNNAH CE: koyi DA fiyayen halitta ne annabi muhammadu (S.A.W.)
8:TSABTA: mace bazaura tana lura da kayan cikin gida. Domin bata son kayan ya lalace.
9:SANIN HAKKOKIN DA YAKE KANTA : tabbas mace bazaura tasan hakkin da yake kanta.
10: GA SAUKIN SADAKI : mace bazaura tana da farashin sadaki Mai sauki kamar yadda hadisin annabi yayi bayani. Yace mafi alkhairin sadaki shine Wanda ba a tsawala ba🤣🤣🤣🤣😋🤣🤣🤣🤣🤣
Saura kuce min mijin hajiya🤣🤣🤣😋😋
©Dr: Barrah Almadany
© Sirrinrikemiji
Post a Comment