Mujallar fim ta Kannywood ta kalubalanci fitacciyar jaruma Rahama Sadau da amfani da mazaunai na roba
Mujallar ta kulabalanci jarumar ne a wani hoton ta da ta wallafa a shafinta watannin baya da suka gabata
– Sai dai jarumar ta fito ta karyata wannan zargi da mujallar take yi mata inda ta nuna cewa na gaske ne bana roba ba
Mujallar fim dai mujalla ce da ta fi kowace kafar sadarwa dake wallafa labaran da suka shafi masana’antar Kannywood dadewa da shahara kasancewar sun fara wallafa mujallar tun shekarar 1999 zuwa yanzu.
Shafin mujallar na Instagram ya wallafa hoton jaruma Rahama Sadau sanye da wasu masu daukar hankali ta juya baya wanda tudun mazaunan ta suka bayyana muraran a hoton kana a kasan hoton suka rubuta ‘real or fake, flesh or rubber’ ma’ana na gaske ne ko na bogi nama ne ko roba.
A wannan zamani da muke ciki an san yadda turawa da wasu daga cikin jaruman kudu kai hadda Hausawan mu musamman mata masu zaman kansu kan kashe makudan kudade wajen zuwa a saka musu mazaunai na roba ko kuma nonuwa kai wasu ma har da gyaran lebe da karan hanci da sauran nau’i na sauya halitta ake musu.
Wannan tambaya ta jawo hankalin mutane inda suka korafin rashin kyautawar irin wannan tambaya da suka yiwa jarumar a cewar wasu hakan kamar cin zarafi ne ko kunyata jarumar suke son yi a matsayin ta na fitacciya.
Sai dai jarumar bata dauka da zafi ba inda ta mayar da martani da harshen turanci take cewa: “na gaske ne alal hakika wannan shi ake kira da girma sai hamdala.”
Ana dai cigaba da nuna rashin dacewar wannan abu da suka yiwa jarumar gami da rokon su da su sauke hoton amma shafin basu amsa kiraye-kirayen jama’ar ba haka zalika jarumar bata nuna damuwarta akan wannan lamari ba, domin kuwa mabiyanta sun fi tada jijiyar wuya kan a goge wannan hoto.
Post a Comment