Shehin Malamin kuma hazikin masanin ilimin kwamfutan ya halarci taron tare da shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar Danbatta, da wasu masu ruwa da tsaki a bangaren sadarwa.
TechEconomy.ng ta bada rahoto a watan Agustan 2019 cewa hukumar NCC ta ce za'a gwada fasahar 5G a Najeriya.
Kalli bidiyon:
Trial Demonstration of 5G Technology in Nigeria. @DrIsaPantami #FMoCDEtoday#FMoCDE19#Experiencethefuture pic.twitter.com/T4NgruCZmD— Fed Ministry of Communications & Digital Economy (@FMoCDENigeria) November 25, 2019
A bangare guda, Ministan sadarwa, Sheikh Dakta Isa Ali Pantami, ya yi gargadi ga wasu marasa kishin kasa dake kokarin yiwa ma'aikatarsa zagon kasa kan ayyukan walwalan jama'an da suke yiwa yan Najeriya.
Malam Pantami, ya yi wannan gargadi ne ta bakin mai magana da yawunsa, Uwa Suleiman, a jawabin da ta saki ranar Litinin a Abuja.
A jawabin yace binciken da aka kaddamar kan wasu masu almundahana ya sa suna kokarin yada labaran karya kan ma'aikatar.
©HausaLoaded
Post a Comment