Ta qara da cewa wannan dalilin yasa ta shirya fim a karkashin kamfanin ta mai suna RARIYA donmin nunawa duniya yadda rayuwar yara ‘yan mata ta ke tafiya a yanzu, sannan iyayen da ba sa saka ido akan ‘ya’yansu su ga yadda rayuwar yara mata ta ke lalacewa a wannan zamani.
Baya ga haka Jarumar ta kara yin kira da babbar murya ga iyayen yara da su ke tura yaran su jami'a ba tare da sun san inda suke sauka ba, kuma su tsaya su yi bincike da irin mutanen da yaran su ke tarayya da su a makaranta saboda zama da marasa tarbiyya na saurin canza wa yara hali.
Ta kuma yi ala wadai ga manyan mutanen da suke boye a gefe guda wadan da ba su da wani aikin da ya wuce suyi lalata da kananan yara ‘yan makaranta ta hanyar ba su manyan kudi saboda su kashe zuciyarsu har su saba musu da irin wannan mummunan halin.
Jarumar ta bayyana jin dadinta ganin yadda sakon fim din nata ya samu isa inda ta ke so ya je. Domin a cewarta mutane da dama a fadin kasar nan harda na kasashen ketare sun kalla sun kuma yaba da irin wannan namijin kokarin da ta yi wajen isar da wannan sakon.
Bayan fitar shirin na ta gidajen talabijin da kasuwa, mutane da damar gaske sun gamsu da sakon da shirin ke dauke da shi, sun kuma koka da yadda al’amura a yanzu suka tabarbare ba tare da an farga ba.
Sai dai kuma duk da wannan hobbasa da Jaruma Rahama Sadau ta yi, ta koka da cewa wannan gudunmawar bai hanata daukar zagi daga wajen mutane ba a duk lokacin da tayi wani dan kankanin laifi. Rahama sadau ta na daya daga cikin matan da suka fi kowa fuskantar qalubale a masana’antar kannywood saboda irin shigar da ta ke yawan yi a duk lokacin da za yi karo a fili ko kuma a shafukanta na soshiyal midiya.
Ko da ya ke duk wata magana da za a yi akanta jarumar bai sa ta mayar da hankalinta a kan su ba ko kuma ta mayar da martani a kan abubuwa da a ke fada ba.
A tattaunawar da akayi da jarumar ta bayyana cewa ita tana koyi ne da gwanar ta fitatciyar jarumar FinaFinan kasar Indiya PRIYANKA CHOPRA kuma duk abinda za a fada akan Priyanka ba ta mayar da martani. Wannan dalili ya saka itama jarumar ba ta tankawa duk wani zagi ko batancin da ake yi mata.
Kwatankwacin hakan ne ya faru wasu makonnin da suka gabata inda wasu mutane su ka hada hotunanta na da da na yanzu; daya sanye da hijabi, dayan kuwa da shiga irin yan matan kudu, abun da a ke ganin ya ci karo da al’adar hausa da kuma addini. Jarumar ta sha suka da jan hankali kwarai daga mutane daban daban a kan shafukan Twitter da Instagram.
Ko da ya ke jarumar ba ta tankawa kowa a kan wannan batun ba, sai dai A ranar 14 ga wannan watan an ga Jarumar ta dora wani rubutu a sashen yayin (status) na WhatsApp mai dauke da sakon gajiya da damuwa da irin tsangwamar da ta ke sha a gurin mutane.
©HausaLoaded
Post a Comment