Northflix ta ruwaito,Fitatcen mai ba da umarni a masana’antar Fina-Finan Hausa ta Kannywood Hassan Giggs wanda yayi fice wajen bada umarnin a kan finafinai irin na suddabaru ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa ya bayyana cewa masana'antar Kannywood na samun cigaba sosai fiye da yadda ta ke a baya.

Daraktan ya bayyana hakan ne a wata zantawar da suka yi da wakilin mu dangane da harkar fim a yanzu. Inda ya fara da cewa Masana’antar kannywood a yanzu kamar jaririya ce sai anyi hakuri wajen rainon ta, amma duk da haka ana kan samun ci gaba fiye da tunanin mai tunani, sannan kuma ana da duk wasu kamarori da na’urori da a ke bukata na amfani a halin yanzu wadan da za su iya yin aikin da ake so. Sai dai ya danganta da irin kudin da mutun zai sanya wajen hanyar wadannan kayan aiki shi ne zai yi tasiri wajen daukakar fim din na sa.

Daraktan ya ba da Misali da lokacin da ya dauki fim din shi mai suna SADAUKI sun samu manyan kamarori da a ka yi aikin da su saboda babban fim ne kuma an kashe kudi sosai tare da manyan jarumai kamar su Adam A Zango, Fati Washa, Abdul M Shareef da sauransu.

Amma Giggs na kyautata zaton cewa nan gaba kadan akwai kamarorin da zasu kawo a fara amfani da su, irinsu RED EPIC, RED DRAGON, BLACK MAC da dai sauransu idan Allah ya ba su iko.

Mun tambaye shi ya ya ke ganin kannywood a bigirar cigaban?

Sai ya amsa da cewa

“Insha Allahu nan da wasu shekaru kadan muna sa ran za mu iya fara gogayya da masana'antun fim na kasashen waje. Saboda muna da mutane wadanda suke da kwazo da kuma daukar sana'ar da mahimmanci. A yanzu dai mu na bukatar masu ilimi ne da masu hannu da shuni da suka saka hannun jari sosai akan harkar,  kuma shigo cikin masana’antar su qara tallafa mata domin tana ciyar da aqalla mutane miliyan biyar wadan da ke ciki da wajen masana’antar.” Inji Daraktan

Tambayar karshe da muka yiwa Daraktan akan yadda ya kake ganin rayuwar ‘yan kannywood a soshiyal midiya?

Bai yi kasa a guiwa ba ya amsa mana cikin raha da nishadi. inda yake cewa “Ko wace masana'anta ta na da na ta salon tafiyar kuma soshiyal midiya an yi ta domin kasuwanci, kowa ya zo ya tallata hajar sa da sauransu, akwai rashin fahimta na dalilin amfani da ita, amma yanzu an fara samun nasara ana zama dai dai, kowa na fahimtar dalilin amfani da soshiyal midiya, da ya ke ba waje ne na cin mutuncin juna ba an yi shi ne domin Sada zumunci da neman kudi ga duk wanda ya fahimta.

Akwai mutanen da su ka yi kudi da social media kuma akwai manyan mutanen da baka taba zato ta dandalin soshiyal midiya su na ganin komai.” Inji Darakta Hassan Giggs

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top