Bambamcin Dake Tsakanin Soyayya Da Mace Mai Kudi Da Auren Mace Mai Kudi

Idan Kana Soyayya Da Mace Mai kudi bata son barinka babu kudi a tare dakai.
 Idan kana auren mace mai kudi bata son ganinka da kudi.
Idan kana soyayya da mace mai kudi bata bari wata ta maka girki kaci. 
Idan kana auren mace mai kudi batada lokacin yi maka girki.
Idan kana soyayya da mace mai kudi alfahari take dakai wajen kawayenta. Idan kana auren mace mai kudin boyewa take ace kai mininta ne.
Idan kana soayya da mace mai kudi duk abunda zatayi mai mahimmanci sai tayi shawara da kai. Ita kuwa mace mai kudi idan kana aurenta boyemaka al'amuranta take yi.
A lokacinda kake soyayya da mace mai kudi tana matukar nunawa 'yan uwanka da iyayenka kauna. Amma idan kana auren mace mai kudi batason ganin naka kusa da ita.
Lokacinda kake soyayya da mace mai kudi, burinta shine duk inda zatayi tafiya kuna tare. Idan kuma kana auren mace mai kudi sai bayan tayi tafiya ma zakaji.
Idan kana soyayya da mace mai kudi, idan zata sakawani aikinta tanayine cikin lanlami da soyayya. Idan kana aurenta kuwa duk abumda zata saka cikin gadara zatayi.

Sai dai kuma wannan binciken ba yana nuna cewa duk mata masu kudi da ake aurensu haka suke ba. Sai dai akasarinsu a lokacinda suke son namiji ya aurensu sunaa da kyankyawan dabi'a da suke canzawa bayan auren.
Yanada da kyau maza musamman samari su fahimci cewa a auren mace mai kudi ba yana nufin namiji zai huta bane kamar yadda wasu suke tunani. Ita mace mai kudi a kullum so take ta samu mijin da bazai shiga rayiwanta ba. Bazai takurawa nemanta ba sai samata idanuwa akan abokan mu'amalanta ba.
Mata masu kudi akasarinsu suna aurene ko domin gudun kada suyi zina ko kuma auren ya karesu daga zargin zina. Mafiya yawansu aure sunayinsa ne a matsayin wani garkuwa na kowacce da nata dalilin yinsa amma ba wai saboda tsabar soyayya da kuma fatan ko tunanin zaman aure ba.
Da fatan maza masu tunanin auren mata masu kudi zasu yi nazari mai zurfi kamin yin hakan.

Tsangayar Malam

---


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top