JARIDAR DIMOKURADIYYA:Wani likita da ya kware a harkar duba lafiyar mata mai suna Olatoye Ogundipe ya bayyana cewa daukar tsawon lokaci a wajen jima’i da yadda ake saduwa ba shine ke sa a haifi mace, namiji ko ‘yan biyu ba.

Ogundipe ya fadi haka ne da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Ilori jihar Kwara.

Ya ce mutane da dama na yawan cewa idan namiji na yawan saduwa da iyalinsa ko kuma yana dadewa a lokacin da ake saduwa da iyalinsa shine zai sa a haifi da namiji ko kuma ‘yan biyu maza, inji PTH

“Wasu mutane na ganin saduwa da mace da rana na sa a haifi ‘ya’yan da suke da nakasa, wasu kuma na ganin cewa mace za ta haifi namiji dake da koshin lafiya idan mijinta ya sadu da ita bayan ta gama jinin haila.

Ogundipe yace duk ire-iren wadannan bayanai shafa labari ne.

Haihuwan ‘ya’ya ya danganta da yadda kwayayen halittar mace da na miji suka garwaye ne.

“ Kwayayen halittan da ke dauke a cikin maniyyin namiji shine ke sa a haifi da namiji ko kuma ‘ya mace. Idan kwan hallita X ya gamu da na mace X a lokacin saduwa to za a haifi mace, idan kuma kwan Y ya gamu da X sai a haifi namiji.

“Kamata ya yi a wayar wa mutane kan game wadannan ilimi saboda adaina rike wasu abubuwa da ba haka ba ana yayadawa.

Ogundipe ya kuma yi kira ga mutane da su rage yawan son doke-dole wai sai sun haifi ‘ya’ya maza.

Idan ba a manta ba a watan Satumba ne sakamakon wani bincike da akayi a jami’ar Newcastle dake kasar Birtaniya ya nuna cewa karfin kwan halittan namiji ne ke sa ma’aurata su haifi da namiji ko kuma ‘ya mace.

Binciken ya nuna cewa lallai idan a zuri’ar mutum mata sun fi yawa to zai fi yawan haihuwar mata ne a cikin ya’yan sa.

Haka kuma idan mazane suka fi yawa a zuri’arsu to zai fi yawan haihuwar ‘ya’ya mata ne.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top