Daga Datty Assalafiy

Wai Zahra Buhari za ta shirya wani taro a Abuja na wayar da kai da fadin tarihin rayuwarta,  kudin shiga dakin taron naira dubu goma (10,000), taron zai gudana ranar Asabar mai zuwa

Na ga ana cecekuce ana kokarin alakanta abin da shugaba Buhari, ita kuma ana zaginta wai Barauniya, babu ruwan shugaba Buhari da wannan taron, haka ne ko ni a gurina kudin ya yi yawa tunda ba lada za a samu da ganin 'yar gidan shugaban kasa ba.

Wannan abu ne mai sauki, ganin damar mutum ne ya ganta, amma maimakon mutum ya kashe naira dubu goma saboda ganin 'yar shugaban kasa ya fi dacewa ya dauki kudin ya kai gidan marayu, idan ba haka ba wannan zai iya zama almubazzaranci.

Sannan Zahra yanzu ba'a karkashin ikon mahaifinta take ba, tana karkashin ikon mijinta ne Ahmed 'dan gidan attajiri Indimi, idan laifi za'a gani sai dai a ga laifin mijinta amma ba shugaba Buhari ba.

Ba Zahra ba wallahi ko shugaba Buhari ne da nake tunanin zan iya sadaukar da rayuwata a kansa zai shirya taro indai sai na biyu dubu goma na ganshi na hakura da ganin nasa a duniya, ma hadu a Aljanna.

Allah Ya shirya.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top