Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Fitacciyar jaruma a cikin masana'antar finafinai ta kannywood Hafsat Idris wadda a yanzu za a iya cewa ta na sahun gaba a cikin matan da ake yayi a masana'antar, ta fadi yadda ta samu matsala a gidan su lokacin da ta bayyana bukatar ta ta shigowa harkar fim a gidan su, kafin daga baya su amince ta.

Jarumar ta bayyana haka ne a lokacin da wakilin mu Mukhtar Yakubu ya ke jin ta bakin ta dangane da matsalar da wasu jarumai su ke samu a gida da zarar sun bayyana bukatar su ta shiga harkar fim.

Wasu daga baya iyayen na su su kan amince, yayin da wasu kuma ba sa samun amincewar ta su, don haka ko dai su bari, ko kuma su ci gaba da yi ba tare da yardar iyayen na su ba.

Kamar yadda Hafsat Idris ta ba mu amsa Cewa " Dole ne duk wadda ta samu kanta a wannan Halin 'Yan Gidansu suji ba dadi.

Amma daga karshe ina nuna musu, wannan fim din fa sana'a ce, sannan idan ka tafi yin shi, waya ma ba ka iya dauka balle ka samu damar zuwa yawo.

Kuma ina so mutane su sani, fim sana'a ce, kuma kowacce sana'a akwai nagari, akwai kuma na banza.

Idan ka tsare kan ka, Allah zai taimake ka, saboda kai dai ka san me ka ke yi, idan ka je iskanci ne to kai ka sani, idan ma ka je a wulakance ne kai ka sani, idan kuma ka je da mutuncin ka Allah zai taimake ka".

Daga karshe ta yi kira ga abokan sana'ar ta da su zamo masu tsare mutuncin su a duk inda su ka samu kan su.

Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top