Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Fitacciyar jaruma Fatima Sadisu wadda aka fi sani da Fati K K, ta bayyana cewa ta dawo harkar fim domin ba ta da wata sana'ar da ta fi ta.

Jarumar ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke tattaunawa da wakilin mu, Mukhtar Yakubu dangane da dawowar da ta yi harkar fim bayan mutuwar auren ta wanda kuma hakan shi ne karo na biyu da Fati din ta kara dawowa fim bayan mutuwar auren na ta.

Domin ko a shekarun baya da ta yi aure, da auren ya mutu Jarumar ta dawo harkar fim ne kafin daga baya ta yi wannan auren, to shi ma a yanzu ga shi ya mutu ta kara dawowa.

Amsar da Jarumar ta ba mu a kan tambayar cewa ta yi "Ba ni da wani abin cewa sai dai in ce Alhamdulillahi, kuma in sha Allahu mu na fatan alheri a ciki.

Da ma can sana'ar mu ce aure ne ya raba mu, yanzu kuma da babu auren mun dawo ka ga ai ba wani abu ba ne, kuma yanzu na tsinci harkar lafiya kamar yadda na bar ta, kuma ina fatan Allah ya zaba mana abin da ya fi alheri.

Amma maganar dawowa fim gaskiya sai a hankali, Saboda za ka ga wasu ba za su fahimce ka ba, amma sana'ar ka sana'ar ka ce.

Komai lalacewar ta ta ka ce ba ka isa ka zage ta ba, saboda da sana'ar aka San ka, da ita ka daukaka, da sana'ar ka ke rufa wa kan ka asiri".

Ta ci gaba da cewa " Amma yanzu mutane su na ganin auren Fati na daya ya mutu, ta kuma kara yin wani ya mutu, ta kuma sake dawowa fim.

Abin da za su fada, shi ne, ai daman ba ta son zaman auren, Fim din ne ya dauke mata hankali, wanda kuma ba haka ba ne wallahi, Inji ta.

Amma ni yanzu gaskiya zabin Allah na ke nema, don haka duk abin da Allah ya zaba wa rayuwa ta ina fatan ya zama alheri a gare ni.

A cikin harkar fim dai ba wani abu ba ne sabo idan mace ta yi aure, kuma bayan auren na ta ya mutu ta kara dawowa cikin harkar.

Sai dai masu lura da al'amuran da ke gudana a cikin harkar fim din su na ganin, duk wata jaruma da ta yi aure ta dawo ba ta kara yin wani tasiri a cikin harkar, saboda irin yadda sababbin jarumai su ke kara shigowa cikin harkar fim din a kowacce rana.

Amma ganin cewar Fati K K jaruma ce mai tasiri a lokacin baya kafin ta yi auren ta na daya da na biyu, ko ita hakan ba zai kasance a gare ta ba?

Sai ta ce " ita dai daukaka ta Allah ce, sannan zuwan wani ba zai hana wani tashe ba, domin kowa zai yi amfani da ta sa basirar ne da Allah ya ba shi.

Saboda haka ni abin da zan ce kawai shi ne Allah ya tabbatar mana da alheri, iya abin da zan iya cewa kenan dangane da dawowa ta harkar fim, inji Fati.

Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top