Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

An dade ba a ganin jaruma Halima Yusif Atete a cikin harkar fim, duk da kasancewar ta babbar jarumar da ta rinka jan zaren ta a baya, domin kuwa ta kai kololuwar da ta zama ita kawai a ke magana a cikin jarumai Mata, amma sai ya zama a yanzu an samu tsawon lokaci ba tare da ana ganin ta ba, duk kuwa da cewar ko da harkar fim din ba ta gudana kamar lokutan baya, to jaruman ba sa rasa yin wani abu da ake ganin motsin su amma ita Halima shiru ake ji.

Wannan ce ta sa mutane su ke tambayar ko dai ta yi aure ne? Hakan yasa Wakilinmu Mukhtar Yakubu ya neme ta domin jin halin da ta ke ciki, in da ta fara yi mana bayani da cewar

"Ina nan a cikin harkar fim, kuma ina gudanar da harkoki na kamar yadda aka sani, sai dai kowa ya sani ita harkar fim ba kamar lokacin baya ba ce, saboda haka ko da ba a ganin mutum to yanayin harkar ne ya zo da haka, don haka mutum ya na bukatar ya duba wani bangaren don ya samar wa kan sa abin rufin asiri, to ina ganin Hakan da na yi ne ya sa mutane ba sa gani na, har ta kai ga su na tambaya, kuma na ji dadi da ba na nan ake tambaya ta Wannan ya nuna cewar mutane sun damu da ni".

Amma ya ya maganar aure,? Don rashin ganin ki ya sa wasu su na cewar ko dai aure kika yi?

To wannan fata ne mai kyau ake yi mini, amma dai ba auren na yi ba ina nan ina jiran lokaci, don ni 'yar sunna ce, da aure aka same ni, don haka ba zan ki aure ba, duk lokacin da ya zo a shirye na ke da na yi, in kai ma ka shirya yanzu haka ma ka fito mu yi!

Idan aure ya zo maka, kawai ka yi shi, Ban ga amfanin a ce Wai don ki na fim ki ki yin aure ba Duk macen da ta ce fim ya fi aure to ta na cikin wahala, don haka mata masu harkar fim su sake tunani.

Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top