- Jarumar ta bude katafaren shagonta na siyar da kayan sawa, kwalliya, gyaran kai tare da gyaran jiki a cikin birnin Kano, Legit na ruwaito.
- Babban dalilin barin masana’antar kuwa shine don ta kasance mai dogaro da kanta tare da samarwa wasu sana’a
Daya daga cikin matasan jaruman masana’antar Kannywood, Rukayya Sukeiman Saje, wacce aka fi sani da Samira Saje, ta bayyana cewa kokarin dogaro da kanta ne yasa ta bar masana’antar shirya fina-finan.
Samira ta bayyana hakan ne a yayin bikin murnar bude sabon shagonta da aka gudanar. An yi bikin ne a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba 2019 a sabon katafaren shagon da mai lamba 148, Titin Lawan Dambazau, daura da filin kasuwar duniya kuma kusa da shagon daukar hoto na Balancy da ke garin Kano.
Jarumar da ta bayyana yadda ta ke son samun hanyar dogaro da kanta, duk da kuwa ta kammala digirinta kuma har ta hidimtawa kasa. Ta ce, ta bar masana’antar ne don ta dogara da kanta tare da taimakawa wajen samar da abin yi ga ‘yan uwanta matasa.
Jarumar ta kara da cewa, in dai a fannin sana’a ne, toh ita kuwa zata iya cewa gado ta yi. Mahaifiyarta ma’aikaciyar banki ce, amma tana dawowa daga ofis take komawa shagonta na dinki inda take sana’a.
Mahaifinta kuwa tun asali bai taba aiki da gwamnati ba.
Samira ta sanar cewa, tana da wani shagon a Katsina. Duk da kuwa na Kanon ya fi girma. Shagon ya kunshi babban falo na siyar da kayan sawa na maza da mata, jakkuna, takalma, agogo da sauransu. Akwai wajen gyaran gashi da kuma wajen gyaran jiki da suka hada da dilka da halawa.
Masoya, ‘yan uwa da kuma abokan arziki duk sun hallara a wajen walimar da aka fara wajen karfe 2 na rana.
Jarumar ta bayyana yadda ta fita daga harkar fim tun a 2016 amma ta ce koda zata koma, ba zata koma ba a matsayin ‘yar wasa. Zata iya komawa a matsayin furodusa ko mai bada umarni, tunda kamfaninta na da rijista kuma mai cin gashin kanshi ne.
©HausaLoaded
Post a Comment