Likitoci wadanda suka kware a bangaren haihuwa a kasar Girka da Sipaniya sun ce sun samo wani jariri ta hanyar kimiyya daga kwayaye na jikunnan mutane uku domin magance matsalar rashin haihuwar wata mata.

An haifi jaririn ne da nauyin kilo 2.9 a ranar talata kuma an bayyana cewa uwar da jaririn suna cikin koshin lafiya.

Likitocin sun ce suna gudanar da wani shiri a likitance wanda ba a taba yin irin shi ba da zai iya taimakon ma'aurata da ke fama da matsalar rashin haihuwa.

Wasu masu sharhi a Birtaniya sun bayyana cewa shirin ya bijiro da cece-kuce da kuma tambayoyi kuma tun farko dama bai kamata a gudanar da shi ba.

Tsarin na gwaji domin dashen kwan haihuwa ana yin sa ne ta hanyar amfani da kwan uwa, da kuma maniyin uba da na wata mata da ta bada kwanta domin taimako.

An kirkiro shi ne domin taimakon ma'aurata da ke fama da cutar ''mitochondrial'' wanda jarirai ke gada daga iyayensu mata.

Sau daya kawai aka taba gwada tsarin, inda aka gwada shi kan wasu ma'aurata da ke kasar Jordan kuma yin hakan ya janyo ce-ce-kuce da dama.

Amma wasu likitoci wadanda suka kware a bangaren haihuwa suna tunanin cewa kimiyya za ta kawo sauki ga tsarin dashen haihuwa.
Wannan duk yana magana kan mitochondria.

A likitance 'mitochondria' abubuwa ne a cikin kwayoyin hallitu na dan adam da ke mayar da abinci wani abu da zai samar da kuzari.

Ana iya gano su a cikin cututtukan mitochondria saboda haka hada kwayoyin halittar mahaifiya da na mai bayar da kwai kyauta da ake kira 'donor', zai iya hana daukar cututuka.

Amma wasu na cewa mitochondria zai iya taimakawa wajen samun ciki ba tare da wata matsala ba duk da cewa har yanzu dai ba a gano gaskiyar hakan ba.

Matar, mai shekaru 32 'yar asalin kasar Girka ce kuma an yi mata tsarin gwaji domin dashan kwan haihuwa sau hudu ba tare da nasara ba.

A yanzu ita uwa ce, amma dan na ta na da kwayoyin halittar matar da ta bayar da kwan ta kyauta a jikin sa.
BBChausa.

Post a Comment

 
Top