Ganyen Mangwaro ya kunshi sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam wajen kawar da wasu cututtuka da suka saba addabar al’ummar musamman a wannan zamani. Ire-iren wannan sunadarai sun hadar da; tannins, anthocyanidins, beta-taraxerol, ethyl acetate da sauransu.

A sakamakon wannan arziki na sunadarai da ganyen mangwaro ya kunsa da kuma tasiran su ga lafiyar dan Adam.

Jerin wasu cututtuka da Ganyen Mangwaro ke warkarwa:


1. Ciwon Suga

Ana amfani da busasshen ganyen mangwaro da aka nike shi ya zama gari wajen magance cutar suga tun a matakinta na farko sakamakon tasirin sunadaran anthcyanidins da kuma beta-taraxerol da ya kunsa.
Kazalika ana kuma jika ganyen magwaro cikin ruwa na kwana guda kana a kwankwadi wannan ruwa domin magance cutar ta suga tun kafin ta ci karfin lafiyar dan Adam.

2. Cutar Hawan Jini

Ganyen Mangwaro ya na da matukar tasiri wajen saukaka cutar hawan jini ta hanyar inganta kuzari na tashoshi da shiyoyi masu aika sakonni na jini.

3. Tsakuwar Koda

Ana amfani da gari na ganyen mangwaro wajen kawar ta wannan cuta sakamakon narkar da tsakuwar koda tare da tsarkake ta daga cututtuka.

4. Cutar Atini

Akan kwankwadi Garin Ganye Mangwaro da aka jika da ruwa wajen samun waraka daga cutar atini ko da kuwa mai zuwa ce da fitar jini.

5. Ciwon Kunne

Akan dumama ruwan da aka tatso daga jikin Ganyen Mangwaro wajen digawa a cikin kunne domin kawar da radadi da cututtuka da suka shafi cikin kunnen dan Adam.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top