Wani sabon bincike ya nuna cewa shaye-shaye abubuwa masu zaki (kayan zaki) kan iya haifar da matsalar bugun zuciya a jikin dan adam, da kuma matsalar gudanar jiki; matsalar da kan iya kawo mutuwa.

Binciken, wanda aka wallafa a shafin ‘sciencedaily.com’ ya nuna cewa, duk lokacin da mutum ya sha kayan zaki, to ya kan kara kusanto da yiyuwar kamuwa da ciwon zuciya, wanda ciwon, zai iya sanadin mutuwarsa.

Domin tabbatar da hakan, masana masu binciken sun yi anfani da mutane dubu 37,716 wurin tabbatar da hakan, inda kuma suka yi a nfani da mata dubu 80,647 domin gane illar ga iyaye masu shayarwa.

Manazartan sun yi duban alakar da ke akwai a stakanin shan kayan zaki da kuma yiyuwar mutuwa ta dalilin hakan.

Binciken nasu, ya nuna cewa, shan kayan zaki fiye da kima hudu ko fiye da haka (kamar irin su Fanta, kokakola da sauran ire-iren kayan zakin dangin su), ya na alaka sosai da mutuwa musamman a cikin mata.

Shugaban da ya jagoranci nazarin, Dakta Vasanti Malik,ya bayyana cewa, “Shan ruwa a maimakon kayan zaki ya fi kara lafiya, hakan kuma ka iya kara sawa a dade a raye.”

Ya ci gaba da cewa, sinadirn ‘diet soda’ zai iya taimaka wa masu dabi’ar shan kayan zaki wurin rage shan su, to amman dai, babu abin da ya kai ruwa karin lafiya.”

Har way au, mazazartan sun bayyana cewa, kara suga a cikin abubuwan sha na kara yiyuwar kamuwa da illar, sannan yana da illoli a jikin dan adam.

“Ba laifi maye gurbin shan kayan zaki da wani abun daban, to amman ga wadanda su ke shan kayan zakihudu ko fiye da haka, to ba zai masu anfani b a kamar wadanda basa sha gabadaya.,” inji manazartan a cikin rahoton.

Sun ci gaba da cewa, “ruwa ba ma wai kawai suna maye gurbin kayan zaki da ke da illa a jikin dan adam ba ne kawai, a’a ai suna ma da matukar anfani a lafiyar dan adam ne, domin suna taimakawa wurin daidai ta bugun zuciya da ayukkan jikin dan adam.”

Ba nan kadai ba, a cewar rahoton, ruwa a jikin dan adama na taimaka masa wurin kara ingancin gabban jikinsa, da kuma taimaka masa wurin fitar da abubuwa maras kyau a jikinsa ta hanyar fitsari, bayan-gari da sauran su.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top