Maza da mata sun dauki zance wani abu ne da mace da namiji za su zauna su yi ta hira na rashin amfani, wasu har ya kai su ga yin wasa da junan su wanda addini ya haramta ko ma zina duka da sunan soyayya.

 Iyaye ku sa ma ‘ya’yan ku ido sosai ta wannan fannin.
Shi dai zance amfaninsa shi ne bawa mace da namiji damar musayan zantuka na soyayya a tsakaninsu, sannan da tattaunawa a kan yanda za su gina rayuwar gidan da suke shirin shiga da kuma fahimtar juna ciki da bai.

Za ka ga a kullum suna tadin awa kusan 6 amma ba su taba zama sun tattauna wasu abubuwa masu muhimmanci ba da yake cikin rayuwar auren da za su shiga ba sai surutan iska, saboda soyayya zalla da surutan banza suke tattaunawa yayin zance, babu fahimtar juna.

Namiji mai tunani da lissafi yana gajerta zantukansa yayin zancen, kuma yana kiyaye tabo zancen da zai kai su ga aikata zina. Maza dayawa yanzu matsalar su kenan, zancen banza da zancen batsa yayin zance, wallahi wannan ba shi ne zai sa ka sami zuciyar macen kirki ba, ba komai kake yi ba illah gayyato shaidan, sai a kiyaye.

Namiji mai hankali zaunar da matar da zai aura yake yi, sannan ya zana mata ra’ayoyinsa, sannan ita ma ta fadi nata a haka za su san junan su, a haka za su gyara in da ya kamata su gyara, kuma a haka ne idan sun ga ba za su iya ba za su rabu kowa ya hakura. Sai ka ga ka yi aure baka fuskantar wani matsala saboda tun a zance kun fahimci junan ku.

Aure fa ba abun wasa bane kamar yanda wasu matasa ke daukan sa ba, kuma ya wuce dukkan tunanin wanda bayyi ya ji yanda yake ba. Zama ne za ka yi da mutum na har karshen rayuwa, ku kwana tare ku tashi tare, dole ka tabbatar da cewa eh ina son wance ne tsakani na da Allah, kuma zan zauna da ita zama na har karshen rayuwata da dadi da ba dadi.

Ka cire duk wasu kyale-kyalen duniya ka kalle ta da ita da dabi’unta da addininta da kuma tarbiyyan da iyayenta suka darata akai, sai ka kwatanta irin zaman da za ku yi domin ku gudu tare ku tsira tare, wannan shi ne ake so mutun in zai yi aure don Allah sai ya duba wannan abubuwan.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top