kwararren mai daukar hoto Mohammed Maikatanga ya dauko hoton wata budurwa mai suna Rahama, wacce a baho ake yawo da ita ana nema mata taimako saboda lalurar nakasta da aka haife ta da shi. Hoto ne da duk mai tausayi idan ya gani sai zuciyar sa ta kadu.

'Yar fim Hadiza Aliyu Gabon na ganin wannan hoto ba tare da bata lokaci ba ta yi tattaki takanas har gidansu a karamar hukumar Wudil ta jihar Kano ta kai mata goma ta arziki, kama daga kayan abinci zuwa manyan kudade. Silar daina yawon bara da Rahama kenan.

A kwanakin baya Naira 500,000 Hadiza Gabon ta bayar kyauta saboda ceto rayuwar mai shirya fina-finai (Alrahuz). Allah Ya jikansa Ya kuma gafarta masa. Wallahi daga attajirai zuwa 'yan siyasa ba kowane zai iya ware wannan kudin ya kyautar saboda ceton ran wani ba.

Tun daga A na Kannywood zuwa Z wallahi babu mai yin irin taimakon da Hadiza Gabon ke yi. Kuma taimakon nata bai tsaya kawai iya farfajiyar Kannywood ba, ta fadada shi zuwa wurare da dama.

Kwararriyar Marubuciya Real Fauziyya D. Sulaiman wacce ta yi fice a fagen taimakon marasa lafiya da marasa gata, ta tabbatar min da cewa Hadiza Gabon na daya daga cikin wadanda ke tallafa musu. (Fauziyya ki yi hakuri na fadi abinda kika fada min a sirri, ina son isar da sako ne)

Hadiza Gabon na daga cikin matan Kannywood da aka fi yawaita Alherinta fiye da sharrinta. Wacce take yawaita murmushi da yawaita kyauta. Amma hakan bai mayar da ita wata waliyyiyar da ba ta kuskure ko ba ta da rauni irin na sauran mutane kamar ni da kai da ke da ita ba.

Abinda ya faru tsakaninta da Amal ta dauki mataki cikin bacin rai wanda daga ta yi nadamar hakan kamar yadda Makusancinta ya fada min.

Amma abin mamaki da takaici sai ga shi an binne dukkan ALHERIN GABON ana ta rura wutar rikicin sai an je kotu. Manyan Zakuna Ali Nuhu Mohammed da Adam A. Zango na kotu, manyan Kannywood na kallo. Yanzu ga babbar Giwar Kannywood, wacce ta zama garkuwar farfado da martabar Kannywood ana shirin tafiya kotu suna kallo.

Ku ci gaba da zuba idon kuna kallo, ai duk wanda ya sha inuwar gemu bai kai ga makogwaro ba. Kamar yadda duk abinda Moda ta samu albarkacin randa ne. Kazalika kifin da ke ruwa baya addu'a ya k'afe. Ganin buzu a Masallaci ya ishi Tunkiya darasi.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top