Daga Sheriff Almuhajir

Ina gani bai kamata mutane su rika capitalizing akan kuskuren mutum su mance da alkairan shi ba, tun bayan abunda ya faru na rikici tsakanin Hadiza Aliyu Gabon da wata yar'uwar ta da suke fim tare wanda aka fahimci komai gaskiyar Hadiza ta yi kuskure da ta dauki mataki a hanunta.

Maimakon a samu hanyar gyara, sai wasu suke amfani da wannan dama domin su saukar da dukkan masifar duniya akan Hadiza, tamkar ita ce ta fi kowa lalacewa a Arewa. Wasu har sun zuga za'a kai ta gaban alkali a gurfanar da ita a daure ta, wasu suna ta jin dadin hakan ta faru. Kamar dama akwai wani gilli da dama yake kwance a zuciyar mutane akan wannan yarinyar.

Na yi rubutu ina yaba wasu halayenta, sai abokaina suke ta muzanta ni me ya sa nace tana da hali nagari? Kuma da za ka bincika laifukan mu da muke ganin ta lalatacciya tsakani da Allah kana iya samu muna aikata duk abunda take aikatawa koma fiye da hakan. Jama'ah mu ji tsoron Allah kar ya tona mana asiri akan alhakin mutane.

Kuma bana janye magana ta, wannan yarinyar a kaf jaruman da suke sana'ar fim babu mai tausayin talakawa, taimakon kanana, Mata, da tsofi kamar ta, ni shaida ne duk shekara tana sadakar dukiya mai yawa lokacin Ramadan, kuma har yanzu akwai talakawan da suke rangwafe a jikinta suke samun saukin kayan rayuwa, Mutum nawa aka baiwa dukiyar talakan suke cinyewa balle ita da take bayarwa daga abunda Allah ya yassare ma ta?

Hakanan a dabi'arta tafi dukkan matan da ke film nutsuwa, ba za ka ganta tana bayyana al-aurarta a fili, ko ka ganta tana badala a gidan biki ba. Kai hatta finafinan da take yi za ka same su da saukin barna ga tarbiyar yara da iyali. To mecece ribar mu idan an daure ko an tozarta ta?

Haba jama'ah kamar dama ana jiran hakan ta faru? Allah ya kiyaye mu daga ciwon zuciya, Amin.






©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top