Shugaba Buhari ya ce "Ta yaya zan yi farin ciki ko in kauda kai da irin wannan kisan rashin imani da barayi ke yi wa al'umma? Ni fa dan adam ne, kuma nasan irin bakin ciki da radadi da yan uwan wadanda aka hallaka suke ciki tare da kuma irin kudaden fansa masu yawa a yan fashin da masu garkuwa da mutanen ke karba a hannun iyalansu"

Shugaba Muhammadu Buhari ya fadi hakan ne yana mai cike da alhini.

Ya kara da cewa "Yadda wasu al'ummar kasar nan ke kokarin saka siyasa a cikin wannan al'amarin yana nuna irin munin bangaren siyasar kasar nan.

"Kusan kowani sati sai na kira jami'an tsaron kasar nan domin su bani bayanin abinda ke faruwa da kuma irin matakan da ake dauka domin kawo karshen irin mummunar kisan gilla da akeyiwa al'umma ba dalili"

Shugaba Buhari ya kara da cewar:

"Babu wani abu da yafi damuna da yafi yanayin tsaro a kasar nan, wanda kusan shine abinda yake mamaye da zuciyata a cikin awanni 24 kullum.  Saboda a matsayina na zababben shugaban kasa,  kare dukiyoyi da rayukan al'umma yana  daya daga cikin ayyukan gwaunatina

"A kullum ina sauraren bayanan jami'an tsaron kasarmu domin insan menene matsalolin da suke fuskanta da kuma bukatotinsu kuma ban taba bata lokaci ba wajen samar musu ababen da suke bukata ba

"Saboda haka,  wadanda suke cewar nayi shiru ko nuna halin ko in kula akan al'amarin ba su ma san me suke yi ba

"Saboda na bada umurnin jibge jami'an tsaro a duk inda keda matsalolin da kuma barayin ke gudanar da ayyukan su na kisan rashin imani ga jama'a

Daga Real Sani Twoeffect Yauri

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top