Wannan yarinyar mai kyau irin na 'dan maciji asalinta 'yar Kasar Kamaru ce, ance a cikin 'yan wasan kwaikwayo na hausawa babu wanda yake burgeta kamar wani katon 'dan rawa kuma 'dan daudu, rana tsaka tayi sallama da iyayenta da suke tare a Kasar Kamaru cewa wai zata zo taga gwaninta, kuma ance wai iyayenta ne ma suka bata kudin mota.

Malam Aliyu Imam Indabawa ya kawo mana cikakken bayani akan wannan yarinya.
Lokacin da ta iso garin Kaduna bata san kowa ba haka tayi tayi ta yawo domin ta samu damar haduwa da 'dan daudun, ta hadu da mutane da dama wanda suke mata karyar zasu kaita wajen gwanin nata, wanda wasu da dama sunyi lalata da ita, wasu har zaman dadiro sunyi da ita, bayan wulakanta kanta da tayi a karshe dai ta sami ganin 'dan wasan wanda ta roke shi ya saka ta a film, sai dai bata cika sharudan film ba, na rashin iya yaren hausa da kwainana sai da ta dauki lokuta kafin ta cika sharudan, wanda dan wasan yayi amfani da hakan yayi ta hada ta manyan mutane suna lalata da ita ana biyanshi.

A halin yanzu wannan yarinya babu abinda take sai bibiyar manyan masu kudi da 'yan siyasa suna lalata da ita suna biyanta, da abinda take samu take rayuwa a inda babu dangin iya balle na baba, da farko tayi zaman haya a hayin Malam Bello Makarfi road Kaduna kasancewar babban gida ne kuma bangarenta daban, wannan yasa tayi ta kawo maza da mata ana fasikanci da shaye shaye, wanda hakan ke taba martabar mutanen gidan, idan suka mata magana sai taci musu mutunci wanda a karshe mai gidan ya gaji ya kore ta, yanzu haka tana rayuwa a unguwar Rimi Kaduna.

Wani abun tausayi ga wannan yarinya shine gata da sunan musulmi amma ko kadan bata sallah, ko azumi yazo bata yi. Shaye shaye kuwa har ruwan kwalba take kurba, cikin shegen data zubar ya wuce a lissafa, kuma har da mata take mu'amala.

Hausawa na cewa" Wanda yasan darajar goro shike lullube shi da algarara" wacce tasan darajar kanta da jikinta itake rufe shi, amma ballagaza wacce ke neman tallata hajarta bude shi take yi kowa ya gani, saboda haka muna gargadin wannan yarinya idan tana cin kasa ta kiyayi ta shuri, ita ba kowa bace sai tsintacciyar mage, wulakantacciya mai bakin iyaye.

Taje tayi ta iskacinta da lalatarta wannan tsakaninta da Allah zai iya gafarta mata ko ya mata azaba, amma abinda ba zamu lamunce ba shine yada hotunan tsiraici domin lalata mana al'umma, kuma dama mun sha fada mafi yawan mutanen nan daga mazinata sai 'yan madigo sai 'yan kwaya, Videon da wata 'yar cikinsu ta saki wai ita Hadiza gabon suna tona asirin junansu ya isa ya tabbatarwa duniya magana ta.

Har ila yau dai, idan har wannan yarinya taci gaba da wannan aika-aika zata ga abinda zai faru da ita, muna da munanan addu'o'i daga kitabu Wassunnah wanda zamu kashe ta dasu alhali tana rayayyiya, ai Zainab Indomie ta isa buga misali, akwai mummunan abu akan wannan ballagaza da ban fadi ba, saboda fadin be dace ba, amma tasan abun kuma idan har wannan abun ya fito sai ta gwammace bata tako kafarta Nigeria ba.

Abu biyu ne zasu saka na fadi, kodai ta karyata zantuka na na sama, ko kuma taci gaba da fasikancin da take aikatawa. A sannan zata gane wannan ma somin tabi ne. Yarinya damu kike zancen dama masu magana kance" Karen bana shine maganin Zomon bana"

Kafin na rufe Zanyi amfani da wannan dama wajen kira ga hukumar tace fina finai kan ta farka daga baccin da take, ta sani cewa akwai sassa na kundin hukumar tace finai finai da suka hana ayi film da macen da ta kawo kanta Industry babu iyayenta ko danginta. idan anyi film da ita haramtacce ne film din, haka nan sashi na 8 sashi na B na karamin kundin wannan hukuma me suna "Arrangement of Section" ya bawa Hukumar tace fina finai damar soke rijistar 'yar wasan da aka samu da aikata laifin rashin da'a ko a daure ta ko aci ta tara.

Abin takaici yau shugaban wannan hukuma ta tace fina finai ya zama kyanwar lami ya bar wadan nan yara suna cin karansu babu babbaka saboda shima dan film ne dan uwansu, yana daure musu gindi suna shegantaka, zaku yarda dani lokacin da Qungiyar Moppan ta dauki hukuncin dakakar da wata mahaukaciyar yarinya ko Rahama Jatau ko Dasau sunanta oho dai! amma dai zaku ganta da katon baki ita nake nufi, a loton aka sami wani sakarai wai shi Ali nuhu ya baiwa Afakallahu Umarnin soke hukuncin, wannan babban abun kunya ne ga Afakallahu.

Muna jan kunnen Afakallu ya shiga taitayinshi ai ya san ko mu su waye, munsan irin dafdala da badakalar dake gudana a hukumar, munsan yadda kake ta rufda ciki akan miliyoyin kudaden gomnat, munsan yadda hukuma ta zamanto tamkar bariki. Karka manta har gobe file din shari'armu dakai yana hukumar Public Complaints (wato) hukumar dake da karfin tsige ka, Mafita kawai kayi abinda dokar hukuma ta umarta idan ba haka ba lamarin ba zai maka kyau ba.

A karshe zamu rufe da nasiha ga wannan yarinya dama abokan aikinta, kuji tsoron Allah mutuwa gaskiya ce, Kwanciyar kabari wajibi ne. Ku aikata mai kyau tun kafin ajalinku ya riske ku, kunsan dai mutuwa bata sanarwa balle sallama, ba ruwanta da yarinta ko lafiya, mutuwar abokan sana'arku kadai zai iya zama muku wa'azi, lokacin daka mutu baka da komai sai aikinka na nan duniya, me zaku fadawa Allah da irin wannan aiki naku na bata tarbiyya da yada alfahsha....? ~Aliyu Imam Indabawa.

Ya kamata iyaye suji tsoron Allah, talauci ba hauka bane, wata kila wannan yarinyar lokacin da take gaban iyayenta ba haka take ba, kar a manta akwai zazzafan hisabi tsakanin iyaye da 'ya'yansu wanda za'ayi a gaban Allah (SWT)

Muna rokon Allah Ya nufi wannan yarinya da shiriya, idan ba zata shiryu ba Allah Ka mana maganinta Amin.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top