Wasu manyan-manyan malaman addinin Musulunci sun yi kira da babbar murya ga Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa da su kawo karshen kisan gillar da ake yi wa jama'a a sassa da dama na Najeriya.
Ko a ranar Asabar an kashe mutane da dama a garin Birnin Gwari na jihar Kaduna, ba ya ga gwamman da ake yi wa kisan gilla akai-akai a jihar Zamfara da wadanda ake sacewa domin neman kudin fansa, abin da ya sa 'yan kasar yin zanga-zanga a ciki da wajenta.
Wannan ya sa malamai da dama yin huduba ta musamman a ranar Juma'ar da ta gabata domin yin Allah-wadai da abin da yake faruwa da kuma neman gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara da su dauki mataki.
"Muna kira ga mahukunta da su tashi tsaye domin kare jama'a da samar musu da zaman lafiya domin hakkin mutane ne a kansu, kuma sai Allah Ya tambaye su," a cewar babban malamin nan na Kano, Dr Sani Umar Rijiyar Lemo.
"Duk wanda ke da [hakkin] ya yi wani abu, to sai Allah Ya tsare shi a ranar gobe kiyama domin ya bayar da bahasi," kamar yadda shehin malamin ya bayyana a shirin Fatawar da ya ke yi a gidan talbijin da rediyo na Rahama.

Fitattun 'yan kasar da dama dai na ci gaba da sukar Muhammadu Buhari da Gwamna Abdul'aziz Yari kan tabarbarewar tsaro musamman a jihar ta Zamfara da kuma Kaduna.

'Hukumomi sun gajiya'

Shahararriyar 'yar jaridar nan Kadariya Ahmed, wacce 'yar asalin jihar ta Zamfara ce, ta ce sakacin 'yan siyasa da rashin iya mulki na neman kashe jihar gaba daya.
"Ko ba komai ya kamata Buhari ya biya ladan halaccin da jama'ar Zamfara suka yi masa na fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin kada masa kuri'a a zaben bana da kuma na 2015," a cewarta.

Sai dai gwamnatin ta sha nanata cewa tana iya kokarinta, inda ta ce ta kaddamar da runduna ta musamman domin yakar 'yan bindigar da ke kashe mutanen.
Suma limaman masallatan Al-Furqan da Imamul Bukhari duka a birnin Kano, Dr Bashir Aliyu da Dr Muhammad Rabi'u Umar, sun yi makamancin wannan kira, inda suka bayyana gazawar jami'an tsaro da gwamnati.
"Ina hukuma take? Ta gajiya, duk tutiyar da ake ta gyara tattalin arziki zancen banza ne idan babu tsaro. Wannan mulkin zai zomanto muku abin kunya da hasara a gareku tun anan duniya, kafin ku tozarta a ranar gobe kiyama," a cewar Dr Bashir.
Ya kara da cewa "noma ya gagara, kasuwanci na neman ya gagara har a birane irin na Kano, mafi yawancin manyan jami'an tsaro duka 'yan arewa ne kuma Musulmai, amma sun kasa katabus".
Ba ya ga Kano, rahotanni sun ce wasu malaman ma a wasu sassan kasar sun yi hudubobi domin Allah-wadai da abin da ke faruwa da kuma jan kunnen gwamnati kan zargin rashin daukar matakan da suka dace.
Ko a ranar Asabar sai da wasu 'yan kasar suka gudanar da zanga-zanga a Abuja suna masu kira ga Shugaba Buhari da ya tashi tsaye kan abin da wasunsu suka bayyana da "sakaci da rikon sakainar-kashin da gwamnatinsa ke wa lamarin".
'Yan Najeriya mazauna birnin Landan ma sun gudanar da makamanciyar wannan zanga-zanga inda suka mika wasika ga ofishin jakadancin kasar da ke can domin a mika wa shugaban kasa suna neman a kawo karshen kashe-kashen.

Me gwamnati take yi?

Ana ta bangaren gwamnatin Najeriya ta sha nanata cewa tana iya kokarinta, inda ta ce ta kaddamar da runduna ta musamman domin yakar 'yan bindigar da ke kashe mutanen.
Shugaba Buhari ya taba zuwa jihar da kansa inda ya kammadar da shirin yakar 'yan bindigar, wadanda ake alakantawa da barayin shanu, sai dai masu lura da al'amura na cewa babu wani sauyi na azo-a-gani da aka samu.
Ana ta bangaren gwamnatin jihar Zamfara ta ce tana bai wa jami'an tsaro wadanda ta ce a karkashin ikon shugaban kasa suke, gudummawar da ta dace.

'A kafa dokar-ta-baci'

Ko a makon da ya gabata, mai magana da yawun Gwamna Yari, Malam Ibrahim Dosara, ya shaida wa BBC cewa suna iya kokarinsu, yana mai cewa babu wata kasa da ke "zaman lafiya a duniya ciki har da Amurka".
Sai dai jama'a da dama na zargin gwamnan da gazawa, abin da ya sa suke kiran a kafa dokar-ta-baci a jihar.
"Watanmu 15 a wannan mambari muna kira a kafa dokar-ta-baci... kafar yadda [Obasanjo] ya yi a jihar Filato a baya, amma an yi burus da mu," a cewar Dr Bashir Aliyu.
Malaman sun kuma ja hankalin jama'a da su guji amfani da duk wasu hanyoyi da suka sabawa addini domin kawo karshen rikicin.
Sannan su koma ga Allah ta hanyar gyara halayensu ko a samu saukin "bala'in da ake fama da shi".
A yanzu dai 'yan kasar sun zuba ido ne domin ganin irin matakan da gwamnati za ta dauka ganin yadda al'amura musamman na tsaro ke kara dagulewa a kasar.


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top