Na lura da yadda tuni mutane suka yankewa Hadiza Gabon hukunci,  a saboda wasu kalamai marasa tushe da Amal ta yada.  Magana ta gaskiya,  kamata yayi Hadiza ta kai kara gun hukuma,  ba wai ta dau hukunci a hannunta ba. A wannan bangare kam, Gabon ta wuce gona da iri. 

To amma,  masu cewa wannan ya tabbatar da zargin da ake mata,  wannan zancen bur ne, in ji tusa.  A dokar musulunci kamar yadda mai Tuhfatul Hukkami ya tabbatar: Wanda duk zancensa ya tsiraita daga zahiri,  to hakkin tabbatarwa yana kansa". Tunda zancen Amal ya tsiraita daga zahiri,  ya zama wajibi ta tabbatarwa duniya da wannan zargi da take wa Gabon, in kuwa ba haka ba,  to hukuncin kazafi ya hau kanta.

Ina mamakin masu hankoran sai sun kore yan film daga musulunci,  yadda suke wa hukunce hukuncen musulunci karan tsaye.  Zargi dai mummunan abu ne a musulunci,  dan ka tsani yan film, da sunan suna bata tarbiya, ba hujja ce a musulunci ka ringa zaginsu da abubuwan da ba haka suke ba. Hasali ma dai,  cewa akayi "ku yiwa mumini kyakkyawan zato " kuma wata karin magana ta larabawa suna cewa "zato zunubi,  koda ya zama gaskiya".

Koda yan film ba muminai bane,  bai kamata ka kallafa musu abinda ba zaka iya tabbatarwa Allah ko hukuma Shi ba.

A tunani,  ya zama wajibi Gabon ta dau mataki na sharia akan Amal,  Amma kuma daga daya bangaren kuma,  Amal na iya neman hakkinta na duka da cin zarafi da Gabon tayi mata.  Wanda in an lura da haka,  to su duka suna da laifi.  Har kullum ya kamata mutane su daina daukar mataki a hannunsu,  kuma lokaci yayi da zamu ja kunnen yan uwa akan yawan jifan musulmai yan uwansu da munanan kalamai.  Wanda kowa yasan haramun ne a musulunci.

Allah yasa mu gane
Fatuhu Mustapha

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top