Fitaccen jarumi kuma Mawaki Garzali Miko, yana shirin bude wani sabon gida wasa na musamman mai zaman kan sa, a garin Azare da ke Jihar Bauchi.

Jarumin yana daya daga cikin jaruman da tauraruwar sa ke haskawa a wannan karnin. Wata majiya ta ce, ya kai akalla wata daya da kwashe kayan sa daga garin Kano, ya koma garin na Azare da zama.

A gobe Asabar, 29 ga watan Fabrairu, ake sa ran za a yi bikin bude gidan wasan, kamar yadda yake ci gaba da wallafa hotunan gayyatar mawaka da 'yan fim a shafin sa na Instagram.

Ana sa ran nan ba da dadewa ba, 'yan fim da mawaka za su ci gaba da halartar gidan domin nishadantar da masoyan su.

Bugu da kari, ba a iya wasannin nishadi gidan zai dogara da shi ba, har Finafinan Hausa wanda ba su fito kasuwa ba, za a rika kaiwa ana haskawa a gidan Galar.

Muna fatan Allah yasa a bude a sa'a.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top