Ambali ya gano haka ne a wani binciken da ya gudanar da sakamakon ya nuna cewa maganin kashe kwari da ake fesawa an hada shi da wasu magungunan da idan aka yawan shaka zai rage karfin gaban mutum da haihuwa ma sai ya gagara.
Sannan kuma ba sai ma an girma ba domin likata yace ko da a ciki ne aka yawaita shakar wannan magani, jariri zai iya samun matsala, sannan kuma da lokacin da yake matashi.
Likitocin kasar Danish sun gudanar da bincike inda suka gano cewa an samu ragowa a haihuwa a duniya gaba da.
Sannan kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta ce bincike ya nuna cewa duk shekara manoma miliyan uku a kasashen dake tasowa na kamuwa da cututtuka da dama a dalilin amfani maginin kashe kwari.
Binciken ya nuna cewa a shekara akan rasa rayukan manoma 250,000 a wadannan kasashe.
Ambali ya ce amfani da maganin kashe kwari na daga cikin matsalolin dake hana a samun abinci dake dauke da sinadarin inganta kiwon lafiya.
Domin gujewa irin wadannan matsaloli likitan ya yi kira ga mutane musamman manoma da su rage yawan amfani da maganin fkashe kwari.jaridar alummata na wallafa.
©HausaLoaded
Post a Comment